-
Siriya : Faransa Ta Sanya Takunkumi Kan Wasu Kamfanoni Da Jami'ai 25
Jan 23, 2018 11:17Kasar Faransa ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu Cibiyoyi da jami'ai su 25 kan zargin taimakawa shirin Siriya na sarafawa da kuma kera makamai masu guba.
-
Qudus : Matakin Trump, Ayyana Karshen Isra'ila Ne _ Nasrallah
Dec 11, 2017 16:08Shugaban Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon, Sayyid Hassan Nasrallah, ya bayyana cewa matakin Trump na Amurka kan ayyana Qudus babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya shelanta kawo karshen Isra'ila ne.
-
Labanon : Hariri Ya Jingine Murabus Dinsa
Dec 05, 2017 17:21Firayi ministan kasar Labanoon, Saad Hariri, ya jingine takardar murabus dinsa, wata guda bayan sanar murabus din tun daga ksar Saudiyya.
-
'Yan Majalisar Tunusiya Sun Soki Sanarwar Bayan Taron Kungiyar Larabawa Kan Hizbullah
Nov 24, 2017 05:15Wani adadi mai yawa na 'yan majalisar dokokin kasar Tunusiya sun yi Allah wadai da sanarwar bayan taron kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa kan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon suna masu kiran gwamnatin kasar da ta janye amincewar da ta yi da sanarwar.
-
Labanon : Bassil, Ba Zai Halarci Taron Kasashen Larabawa Ba Kan Iran
Nov 19, 2017 10:05Ministan harkokin waje na kasar Labanon, Gebrane Bassil, ba zai halarci taron kungiyar kasashen larabawa ba da Saudiyya ta kira kan Iran.
-
Basil: Ba Mu Da Shakku Cikin Cewa Hariri Yana Cikin Mawuyacin Hali
Nov 16, 2017 05:42Ministan harkokin wajen kasar Labanon, Gebran Bassil, ya bayyana shakkunsa dangane da halin da firayi ministan kasar Sa'ad Hariri yake ciki a kasar Saudiyya yana mai cewa ci gaba da zaman Haririn a Saudiyya ba tare da dawowa gida ba wani lamari ne mai ban mamaki da tada hankali da ke nuni da cewa lalle ba dai lafiya ba.
-
Labanon : Ana Ci Gaba Da Matsin Lamba Ga Saudiyya Kan Tsare Hariri
Nov 15, 2017 16:11Shugaban Michel Ayun, na Labanon na kara matsin lamba ga Saudiyya bisa zarginta da ci gaba da tsare firayi ministan kasar ta Labanon Saad Hariri.
-
Faransa Ta Baiwa Mahukuntar Birin Riyad Wa'adin Karshe Na Sakin Hariri Ya Koma Kasar Sa
Nov 14, 2017 18:58Majiyoyin labaran kasar Faransa sun habarta cewa shugaban kasar ya bawa mahukuntan saudiya wa'adin karshe na barin piraministan kasar Labnon ya koma kasar sa.
-
Wani Dan Gwagwarmaya A Kasar Aljeriya Ya Zargi Mahukuntan Saudiyya Da Hada Kai Da H.K.Isra'ila
Nov 14, 2017 06:18Daya daga cikin 'yan gwagwarmayar Aljeriya da suka yi yakin 'yantar da kasar daga mulkin mallakar kasar Faransa, kuma mamba a kungiyar National Liberation Front ta kasar ya bayyana cewa: Mahukuntan Saudiyya sun hada kai ne da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da nufin wanzar da bakar siyasarsu a yankin gabas ta tsakiya.
-
Hizbullah: Saudiyya Tana Son Ta Maimaita Yadda Ta Yi Wa Katar Akan Kasar Lebanon
Nov 13, 2017 18:57Shugaban majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah Sayyid Hashim Safiyyudin ya zargi Saudiyya da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Lebanon.