Pars Today
A yayin da Dakarun sa kai na Hashadu-Sha'abi suka isa kan iyakar kasar Iraki da Siriya dake yammacin jihar Nainuwa na arewacin kasar, Firaminstan kasar Haidar Abadi ya shiga birnin Mausil babban birnin Jihar Nainuwa a marecen wannan Litinin.
A jiya alhamis ne Amurkan ta sanar da kashe fiye da fararen hula 100 a gundumar Nainawa.
Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta aiwatar da kisan gilla kan wasu fararen hula da ta kama suna kokarin tserewa daga yankin Assirajkhanah da ke yammacin garin Mosel domin tsira da rayuwarsu.
Dakarun hadin gwiwa masu yaki da ayyukan ta'addanci a Iraki sun samu nasarar halaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan takfiriyya na ISIS a yammacin birnin Mausul.
Dakarun kasar Iraki da suke samun daukin dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar kwato kimanin kashi 90% na yammacin garin Mosul a kokarin da suke ci gaba da yi na fatattakan 'yan ta'addan kungiyar Da'esh (ISIS) daga garin na Mosul wanda shi ne gari na biyu mafi girma a kasar.
A jiya alhamis sojojin Iraki sun kasar samun nasarar kwace wani unguwanni biyu a cikin birnin Mosel.
Kakakin Ma'aikatar cikin gidan kasar Iraki ya ce bayan 'yanto bangaren gabashin Mosil kashi 83% na Mosil an tsarkake shi daga hanun 'yan ta'addar ISIS
Sojojin Kasar Iraki sun kai hari ne akan wani taro da 'yan kungiyar Da'esh su ke yi a tsakiyar garin Tala'afar da ke yammacin birnin Mosel.
Ma'aikatar tsaron kasar Iraki ta sanar da cewa a halin yanzu dakarun kasar sun gama yin kawanya wa 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a yammacin garin Mosul, tungar karshe ta 'yan kungiyar a kasar Irakin.
Dakarun gwamnatin Iraki da sauran dakarun sa kai na al'ummar kasar suna ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan ISIS (Daesh) a yammacin birnin Mausul.