Pars Today
Dakarun hadin gwiwar Iraki sun hallka sama da 'yan ta'addar ISIS 50 a garin Tal'afar na yammacin Mausil
Dakarun Gwamnatin Iraki sun samu nasarar kwace filin jirgin sama na garin Mausil daga hanun 'yan ta'addar ISIS.
Dakarun sa kai na kasar Iraki sun samu nasarar tsarkaka wani kauye daga kewayen garin Tal'afar dake yammacin garin Mausil.
Sojojin kasar Iraki da suke samun goyon bayan dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar kwato wasu garuruwa da suke wajen garin Mosul bayan kaddamar da farmakin karshen a jiya Lahadi da nufin kwato Yammacin garin Mosul din da ya rage a hannun 'yan ta'addan kungiyar Da'esh (ISIS).
MDD ta nuna damuwa kan mawuyacin hali da mazauna yammacin garin Mausil na kasar Iraki ke ciki.
Jiragen yakin Iraki sun kashe 'yan kungiyar Da'esh masu yawaa gundumar Nainawa a yau asabar.
Ma'aikatar tsaron Iraki ta sanar da kashe 'yan kungiyar Da'esh da dama a gabacin birnin Musel.
Majiyar tsaron Iraki ta sanar da halakan 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da dama ciki har da mataimakin shugaban kungiyar Abubakar Bagadadi a harin da jiragen saman yakin sojin kasar suka kaddamar kan sansanin 'yan ta'addan.
A ci gaba da fatattkar 'yan ta'addan ISIS da dakarun kasar Iraki ke yi a gundumar Nainawa, a yau sun killace adadi mai yawa na 'yan ta'adda a yammacin birnin Mausul, babban birnin lardin Nainawa.
Rahotanni daga kasar Iraki na nuni da cewa sojojin kasar na kusa da kwace kogin Dijlah (Tigris) da ya ratsa tsakiyar garin Mosul lamarin da ya ke ci gaba da tilastawa 'yan ta'addan Daesh ja da baya a kokarin da sojojin suke yi na kwace garin daga hannun 'yan ta'addan.