Dakarun Iraki Sun Tsarkake Wasu Yankuna A Yammacin Mausul Daga ISIS
Dakarun hadin gwiwa masu yaki da ayyukan ta'addanci a Iraki sun samu nasarar halaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan takfiriyya na ISIS a yammacin birnin Mausul.
Tashar talabijin ta al'alam ta bayar da rahoton cewa, a yau dakarun Iraki sun samu gagarumar nasara wajen kwace wasu karin yankuna tare da tsarkake daga 'yan ta'addan ISIS a ayammacin birnin Mausul, inda a halin a an 'yan ta'addan suka yi saura.
'Yan ta'addan na ISIS da suke samun dauki daga Amurka da Saudiyya da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa, suna garkuwa da dubban fararen hula a cikin yankunan yammacin birnin Mausul, wanda hakan ne yasa ala tilas dakarun na Iraki su rika yin taka tsan-tsan, domin kaucewa hasarar rayukan fararen hula a yankin.
Baya ga haka kuma majiyoyin tsaro a Iraki sun tabbatar da cewa, 'yan ta'addan na ISIS suna da tarin makamai masu guba a hannunsu, wadanda a kowan elokaci za su iya yin amfani da su domin kashe dubban mutane a yankin.