-
Majalisa ِDattawan Nijeriya Ta Amince Da Sunayen Jakadu 45, Da Watsi Da Wasu Guda Biyu
Mar 23, 2017 12:03Majalisar Dattijan Nijeriya ta tantance da kuma amincewa da sunayen jakadu guda 45 cikin guda 47 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu da su a matsayin jakadun da yake son turawa kasashe waje, to sai dai sun yi watsi da wasu 2 daga cikinsu.
-
Jerin hare-haren ta'addanci a Najeriya
Mar 23, 2017 06:33Wasu Mutane da ba a san ko su waye ba sun kai wasu jerin hare-haren ta'addanci a Jihar Benue dake kudu maso gabashin Najeriya.
-
Harin Bam ya hallaka Mutane 4 a Sanasanin 'yan gudun hijra
Mar 22, 2017 07:54Wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a sansanin 'yan gudun hijra na arewa maso gabashin Najeriya.
-
Kamaru Na Cilastawa 'Yan Gudun Hijira Najeriya Komawa Gida
Mar 22, 2017 00:52Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce Kamaru na amfani da karfi wajen mayar da 'yan gudun hijira Najeriya da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu gida.
-
'Yan Sanda A Nijeriya Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 46 Yayin Rikicin Ile-Ife
Mar 21, 2017 01:53Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewar mutane 46 ne aka kashe kana wasu 96 kuma suka sami raunuka sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Yarbawa da Hausawa a garin Ile-Ife na jihar Osun da ke kudancin Nijeriya.
-
Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Harin Kunar Bakin Wake A Kusa Da Maiduguri
Mar 19, 2017 07:45Kakakin rundunar 'yan sandan Nijeriya ya tabbatar da cewa mutane hudu sun mutu kana wasu guda takwas kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake da wasu 'yan ta'adda su uku suka kai wani kauye da ke kusa da garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
-
Gwamnatin Nijeriya Za Ta Hukunta Wadanda Suke Da Hannu Cikin Rikicin Ile-Ife
Mar 17, 2017 05:55Ministan cikin gidan Nijeriya Janar Janar Abdurrahman Bello Dambazau (RTD) ya bayyana cewar gwamnatin kasar za ta hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin rikicin da ya faru a garin Ile-Ife da ke Jihar Osun da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 40.
-
Mukadashin Shugaban Kasar Najeriya zai ci gaba da jan ragamar milkin kasar
Mar 10, 2017 14:33Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da hutawa bayan ya koma gida daga jinyar makwanni bakwai da ya yi a Birtaniya.
-
Hukumar Zaben Nijeriya Ta Fitar Da Jadawalin Zabubbukan Shekara ta 2019 A Kasar
Mar 10, 2017 02:54Hukumar zabe ta Nijeriya (INEC) ta fitar da jadawalin zabubbukan da za a gudanar a kasar a shekarar 2019 da suka da na shugaban kasar, gwamnoni da na 'yan majalisu.
-
A Yau Ne Ake Sa Ran Shugaba Buhari Zai koma Nijeriya
Mar 10, 2017 02:16A wani lokaci a yau din nan Juma'a ne ake sa ran shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai koma gida Nijeriya bayan hutu da kuma jinyan da yayi a birnin London na sama da wata guda.