Mukadashin Shugaban Kasar Najeriya zai ci gaba da jan ragamar milkin kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18404-mukadashin_shugaban_kasar_najeriya_zai_ci_gaba_da_jan_ragamar_milkin_kasar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da hutawa bayan ya koma gida daga jinyar makwanni bakwai da ya yi a Birtaniya.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Mar 10, 2017 14:33 UTC
  • Mukadashin Shugaban Kasar Najeriya zai ci gaba da jan ragamar milkin kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da hutawa bayan ya koma gida daga jinyar makwanni bakwai da ya yi a Birtaniya.

Da yake magana ga manyan jami'an gwamnatinsa a birnin Abuja,Shugaba Buhari  ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da jan ragamar al'amura, saboda ya nada bukatar karin hutu, sai dai ba a bayyana ko zuwa wani Lokaci ne mukaddashin Shugaban kasar zai ci gaba da jan ragamar milkin kasar

Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ke damun shugaba Buhari,  amma jami'ansa sun nace cewa babu wani abin damuwa a cikin lamarin.

Shugaba Buhari ya ce "Yana samun sauki sosai" amma ya kara da cewar yana bukatar ayi masa wasu karin gwaje-gwaje.

A ranar 19 ga watan Janairun 2017 din da ta gabata ne, Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya tafi birnin Landon na kasar Birtaniya domin gudanar da hutu na kwanaki goma, to saidai bayan karewar hutunsa  ya rubutawa Majalisa wasikar neman kara wa'adin hutunsa domin duba lafiyarsa, lamarin da ya janyo cece-kuce a cikin kasar.