Pars Today
Kasar Qatar ta bukaci tattaunawa da Saudiya da kawayenta bayan da kasashen suka yanke duk wata irin hulda da ita bisa zargin taimakawa ayyukan ta’addanci.
Bayan da wasu kasashen Larabawan yankin tekun Pasha suka dauki matakin yanke alakar jakadancinsu da kasar Qatar, kasashen Masar da Libiya ma sun rufa musu baya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kira ga dukkanin makobtanta da suke kudancin yankin tekun Pasha da su dauki darasi daga mummunan yana yin da yankin ke ciki domin dawowa cikin hankali da tunaninsu da nufin ganin an samu zaman lafiya a yankin.
Gwamnatin kasar Qatar Ta Musanta Zargin Wasu Kasashen Larabawa Na cewa tana shisshigi cikin lamaran wasu kasashe a yankin ko kuma tana goyon bayan yan ta'adda.
A yau Litinin gwamnatocin kasashen Saudiyyah, Bahrain, UAE da kuma Masar, sun sanar da yanke alakarsu da kasar Qatar.
Wani Dan Majalisar Dokokin Masar yace ya zama wajibi a kalubalanci ta'addancin da kasashen Qatar da Turkiya ke ci gaba da aikatawa a yankin gabas ta tsakiya.
Wani dan Majalisar Dokokin Kasar Masar ya zargi kasashen Turkiyya da Qatar da hannu a ruruta wutan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya tare da bayyana su a matsayin maha'inta.
Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Libya sun zargi gwamnatocin kasashen Qatar da Turkiya kan mara baya ga 'yan ta'addan takfiriyya da suka addabi al'ummar kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta mayar da martani ga gwamnatin kasar Qatar dangane da hukuncin da wata kotun kasar Masar ta yanke wa hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi kan zargin da ake masa na leken asiri wa kasar Qatar din.