Qatar Ta Bukaci Tattaunawa Da Saudiya Da Kawayenta
Kasar Qatar ta bukaci tattaunawa da Saudiya da kawayenta bayan da kasashen suka yanke duk wata irin hulda da ita bisa zargin taimakawa ayyukan ta’addanci.
Gidan talabijin din kasar na Al' Jazeera ne ya rawaito ministan harkokin wajen kasar, Mohammed bin Abdul Rahman na fadan hakan, inda ya ce Qatar a shirye take domin tattaunawa ta gaskia da makoftanta na yankin tekun fasha domin ganin an kawo karshen wannan mastala.
Mista Abdul Rahman ya kara da cewa lamarin ba zai kai ga dagulewar al'amura ba tsakanin kasarsa da dadadun abokan huldarta ba.
Ya ce lalle akwai batutuwan da suke da sabani akansu, amman huldar dake tsakaninsu ta fi sabanin yawa.
Da sanyin safiyar jiya ne dai kasashen da suka hada da Saudiya, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabwa da Yemen da Masar suka sanar da yanke huldar diplomasiya da harkokin kasuwanci da rufe iyakoki na sama da kasa da na ruwa tsakaninsu da Qatar, bisa zarginta da taimakawa kungiyoyin 'yan ta’adda irinsu Al 'Qaeda da kungiyar IS, zargin da Qatar din ta musunta da cewa marar tushe ne.
Kasashen Iran, Amurka da Turkiyya dai sun kira kasashen dasu kai zuciya nesa, duba da rikice-rikicen da yankin ke fama da shi.