Saudiyya, UAE, Bahrain, Masar, Sun Sanar Da Yanke Alaka Da Qatar
(last modified Mon, 05 Jun 2017 06:33:40 GMT )
Jun 05, 2017 06:33 UTC
  • Saudiyya, UAE, Bahrain, Masar, Sun Sanar Da Yanke Alaka Da Qatar

A yau Litinin gwamnatocin kasashen Saudiyyah, Bahrain, UAE da kuma Masar, sun sanar da yanke alakarsu da kasar Qatar.

Gwamnatocin wadannan kasashe 4 sun sanar da hakan ne bisa abin da suka kira mara baya ga kungiyoyin 'yan ta'adda da Qatar ke yi, wadanda suke barazana ga Saudiyya da kuma sauran kasashen larabawa na yankin.

Haka nan kuma Saudiyya ta sanar da fitar da Qatar daga abin da take kira kawancen larabawa da ke yaki da kasar Yemen, wanda Saudiyya ta kafa kuma take daukar nauyinsa da kuma jagorantarsa.

Baya ga haka kuma wadannan kasashe sun sanar da dakatar da dukkanin tafiye-tafiye na jiragen sama da kasa da kuma ta ruwa daga kasashensu zuwa Qatar, ko kuam daga Qatar zuwa kasashenssu.

Wannan mataki dai ya zo ne makonni biyu bayan ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump ya gudanar a birnin Riyadh fadar mulkin masarautar Al Saud, inda ya hada dukkanin shugabannin wadannan kasashe, da nufin hada kansu domin shelanta yaki a kan kasar Iran.