-
Saudiyya: A Yau Ne Aka Cika Shekaru 3 Da Kisan Sheikh Nimr Baqir Nimr
Jan 02, 2019 17:17A yau ranar 2 ga watan Janairu 2019 aka cika shekaru 3 da kisan gillar da masarautar Al Saud ta yi wa Sheikh Nimr Baqir Nimr.
-
Shugaba Macron Ya Jaddada Wajibcin Gudanar Da Bincike Na Kasa Da Kasa Kan Kashe Khashoggi
Dec 01, 2018 05:23Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana wajibcin gudanar da bincike na kasa da kasa dangane da kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi, dan jarida dan kasar Saudiyya mai suka gwamnatin kasar, da aka yi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
-
Amurka Ta Wanke Yariman Saudiyya Daga Kisan Kashoogi
Nov 14, 2018 06:29Babban mai bada shawara akan harkokin tsaron ga Shugaban kasar Amurka, John Bolton ya ce; Kwararru da su ka saurari faifen sauti na kisan da aka yi wa Kashoogi sun ce babu wani dalili da yake nuni da cewa yarima mai jiran gado yana da hannu a ciki
-
Rahoto: Yunkurin Saudiyya Na Rusa Tattalin Arzikin Iran Da Kashe Wasu Manyan Jami'anta
Nov 13, 2018 05:34A cikin wani rahoto da jaridar New York Times ta buga, ta fallasa wani boyayyen shiri da gwamnatin Saudiyya take da shi kan rusa tattalin arzikin kasar Iran, da kuma yi wa wasu daga cikin manyan jami'an kasar ta Iran kisan gilla, musamman ma janar Qasem Sulaimani, babban kwamandan rundunar Quds, reshen dakarun kare juyin juya hali da ke gudanar da ayyuka awajen kasar ta Iran, wanda ya taka gagarumar rawa wajen karya lagon 'yan ta'addan takfir masu da'awar jihadi a kasashen Syria da Iraki.
-
Masar Ta Ce Ta Kame Wasu Gungun Mutane Da Suke Shirin Kashe Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya
Nov 12, 2018 18:57Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame wani gungun mutane 20 da suke shirya makarkashiyar aiwatar da kisan gilla kan yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman.
-
An Fallasa Wani Makircin Da Gwamnatin Saudia Ta Kullawa Iran
Nov 12, 2018 11:44Jaridar New York Time ta kasar Amurka ta nakaltu majiyar jami'an tsoro kusa da yerima mai jiran gadon kasar Saudiya dangane da shirin kashe biliyoyin dalar Amurka don rikita kasar Iran.
-
Saudiyya Za Ta Hanawa Palasdinawa Miliyan 3 Aikin Haji
Nov 09, 2018 19:07Tashar talabijin din al'alam ta bada labarin cewa; Kasar ta Saudiyya wacce ta hada kai da haramtacciyar Kasar Isra'ila ta hana ba da visa ga Palasdinawa miliyan 3 da suke a kasashen Jordan, Lebanon da gabacin birnin Kudus da Paladinu dake karkashin mamaya
-
Hazim: Saudiyya Ta Kashe Jamal Khashoggi Ne Domin Tsoron Fallasa Asiranta
Nov 05, 2018 06:22Daraktan jaridar Alfajr ta kasar Aljeriya Haddad Hazim ya bayyana cewa, mahukuntan kasar Saudiyya sun dauki matakin kashe Jamal Khashoggi ne domin tsoron kada ya fallasa asiransu da ya sani.
-
Kokarin Amurka Na Fitar Da Saudiyya Daga Cikin Kangin Tsaka Mai Wuya Da Ta Shiga A Yamen
Nov 01, 2018 05:23Sakamakon matakan matsin lamba da kasashen Amurka da Saudiyya suke fuskanta tun bayan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya mai adawa da masarautar kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi, mahukuntan Amurka suka fara batun neman hanyar warware rikicin kasar Yamen.
-
A. Larijani: Gwamnatin Saudiyya Ita Ce Ummul Aba'isin Matsalolin Da Duniyar Musulmi Suke Ciki
Oct 22, 2018 18:11Alkalin alkalai kana shugaban Ma'aikatar shari'a ta Iran, Ayatullah Sadiq Amoli Larijani ya bayyana cewar mahukutan Saudiyya suna amfani da kudaden da suke samu daga man fetur wajen haifar da matsaloli masu yawan gaske ga al'ummomin kasashen Afghanistan, Pakistan, Iraki, Siriya, Labanon da wasu kasashen Afirka.