Amurka Ta Wanke Yariman Saudiyya Daga Kisan Kashoogi
Babban mai bada shawara akan harkokin tsaron ga Shugaban kasar Amurka, John Bolton ya ce; Kwararru da su ka saurari faifen sauti na kisan da aka yi wa Kashoogi sun ce babu wani dalili da yake nuni da cewa yarima mai jiran gado yana da hannu a ciki
Tashar talabijin din CNBC ta Amurka ta ambato babban jami'in tsaron kasar yana ci gaba da kare mahukuntan Saudiyya da nesanta su daga kisan da aka yi wa dan jaridar kasar Jamal Kashoogi a cikin karamin ofishin kasar da yake a birnin Istanbul na kasar Turkiya
Shi kuwa shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya ce; Kisan da aka yi wa Kashoogi ya kasance ne bisa umarni shugabannin Saudiyya kai tsaye, don haka Ankara take son ganin an bayyana sunayen wadanda su ka ba da umarnin hakan.
A farkon watan Oktoba ne aka kashe dan jaridar na Saudiyya jamal Kashoogi a cikin karamin ofishin jakadancin kasar da yake a birnin Istanbul na turkiya.
Saudiyya tana zargin Saudiyya da rashin ba da hadin kai a binciken da take yi na kisan dan jaridar