Saudiyya Za Ta Hanawa Palasdinawa Miliyan 3 Aikin Haji
(last modified Fri, 09 Nov 2018 19:07:30 GMT )
Nov 09, 2018 19:07 UTC
  • Saudiyya Za Ta Hanawa Palasdinawa Miliyan 3 Aikin Haji

Tashar talabijin din al'alam ta bada labarin cewa; Kasar ta Saudiyya wacce ta hada kai da haramtacciyar Kasar Isra'ila ta hana ba da visa ga Palasdinawa miliyan 3 da suke a kasashen Jordan, Lebanon da gabacin birnin Kudus da Paladinu dake karkashin mamaya

Jaridar Ha'aretz ta 'yan sahayoniya ta buga labarin da yake cewa; Saboda kusanci da ake samu a tsakanin Saudiyya da Isra'ila, palasdinawan da suke da pasport din Isra'ila ne kadai za su sami yin aikin haji

A can kasar Jordan, ma'aikata mai kula da al'murran addinin musulunci ta ce; Saudiyya ta bukace ta da kada ta bai wa kowace Bapalasdine passport na musamman da ta saba yi domin aikin haji

Tun daga 1978 ne Jordan take yi wa Palasdinawa 'yan gudun hijira passporta na musamman domin yin aikin haji

Sabon matakin Saudiyyar dai yana a karkashin aiwatar da manufar Amurka ne ta yarjejeniyar karni wacce take nufin kawar da batun hakkin palasdinawa na komawa kasarsu ta gado.