Pars Today
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da gagarumin rinjaye kan kudurin da ya bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya janye matsayarsa ta sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
A wannan Alhamis babban zauren MDD ke wani zaman gaggawa, inda kuma za'a kada kuri'a kan nuna adawa da matakin shugaba Trump na Amurka na ayyana birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin yahudawa sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Matakin da gwamnatin Amurka ta dauka kan birnin Qudus mataki ne mai tsananin hatsari.
Kungiyar kasashen Larabawa ta yi Allah wadai da hawan kujeran na ki ko kuma Hakkin Veto a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a ranar litinin don hana kudurin kare birnin Qudus wanda kungiyar ta gabatar.
Shugaban jam'iyyar Nahdha ta kasar Tunisia Rasheed Al-ghanushi ya ce batun Qudus ne zai zama mahadin kan al-ummar musulmi.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da hawa kujerar nakin da Amurka ta yi dangane da kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniay da ya bukaci Amurkan da ta janye sanarwar da ta yi na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kasar Amurka ta hau kujeran naki dangane da wani kuduri da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya so fitarwa a daren jiya da nufin kiran gwamnatin Amurka da ta janye matsayar da ta dauka na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kwamitin Tsaron MDD ya fara gudanar da bincike kan koken da kasar Masar ta shigar na watsi da sabon kudirin shugaban kasar Amurka Donald Trump kan birnin Qudus.
Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun sake jaddada matsayarsu ta kin amincewa da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kungiyar hadin kan majalisun kasashen larabawa ta sanar da cewa a gobe Alhamis za ta gudanar da wani taro na gaggawa a kasar Morocco don tattauna matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.