Pars Today
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yayi kakkausar suka ga matsayar da shugaban Amurka Donald Trump na sanar da Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila yana mai cewa babu abin da hakan zai haifar in ban kirkiro wani sabon rikici a yankin Gabas ta tsakiya.
Jakadun wasu kasashen Larabawa sun fitar da daftarin kuduri kan matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka dangane da birnin Qudus suna neman tsoma bakin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da babban zauren Majalisar.
Babban kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a Iran (IRGC) ya bayyana cewa rundunarsa a shirye take ta tallafawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawan Sahyoniya a Palasdinu.
Shugaban Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon, Sayyid Hassan Nasrallah, ya bayyana cewa matakin Trump na Amurka kan ayyana Qudus babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya shelanta kawo karshen Isra'ila ne.
Tsohon ministan harkokin waje na Vatican Pietro Parolin ya bayyana cewa matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka kan birnin Quds zai kara rikita harkokin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ne.
Jami'ar Azhar ta kasar Masar ta yi gargadi kan irin mummunan hatsarin da ke tattare da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, don haka ta bukaci shirya zaman taron kasa da kasa kan batun na Qudus.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana cewa: Shugaban Amurka Donald Trump ya shawarci kawayen kasarsa a yankin gabas ta tsakiya kafin daukan matakin shelanta Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Da safiyar yau lahadi ne kasashen taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa ya fitar da bayani da ya kunshi yin tir da matakin shugaban kasar Amurka akan birnin kudus
Paparoman Kibdawan kasar Masar, Paparoma Tawadros II ya soke shirin ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da a baya aka shirya yi a wani lokaci a watan nan a birnin Alkahira don nuna rashin amincewarsa ga matsayar da shugaban Amurkan ya dauka na bayyanar birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila tana mai sake jaddada goyon bayanta ga kafa kasar Palastinu mai cin gashin kanta.