Bayanin Bayan Taron Kasashen Larabawa Akan Kudus
(last modified Sun, 10 Dec 2017 07:34:57 GMT )
Dec 10, 2017 07:34 UTC
  • Bayanin Bayan Taron Kasashen Larabawa Akan Kudus

Da safiyar yau lahadi ne kasashen taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa ya fitar da bayani da ya kunshi yin tir da matakin shugaban kasar Amurka akan birnin kudus

Bayanin ya ci gaba da cewa matakin na shugaba Donald Trump dangane da birnin kudus, zai haddasa rikici da tashin hankali ne a cikin yankin gabas ta tsakiya,sannan kuma yana cin karo da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.

Bugu da kari ministocin harkokin wajen na larabawa sun kira yi shugaban na kasar Amurka da ya janye matsayarsa akan birnin na Kudus.

A farkon taron, babban sakaraten kungiyar hadin kan kasashen larabawan Ahmad Abul Ghaid  ya gudanar da jawabi da ya bayyana abinda ya faru da fitina, wacce kuma bai kamata a yi shiru akanta ba.