Dec 21, 2017 10:30 UTC
  • MDD Na Zaman Gaggawa Kan Batun Kudus

A wannan Alhamis babban zauren MDD ke wani zaman gaggawa, inda kuma za'a kada kuri'a kan nuna adawa da matakin shugaba Trump na Amurka na ayyana birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin yahudawa sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.

Zaman dai na gudana ne a yayin da Amurka ta yi barazanar katse tallafin da take bayarwa kan duk kasar data ki amuncewa da matakin na Trump a MDD.

A babban zauren majalisar inda kasashe 193 zasu kada kuri'a, babu kuri'ar naki da ake bukata, kamar yadda Amurkar ta yi a yayin da aka gabatar da kudirin gaban kwamitin tsaro na MDD.

Wasu kasashen Larabawa da kuma na musulmai ne suka bukaci zaman na Majalisar dinkin duniya.

A wani labari kuma dake shigowa tuni Isra'ila ta bakin fira ministan ta, Benjamin Netanyahu ta yi watsi da sakamakon taron koli na MDD, tun kafin aje ko ina, yana mai danganta zauren majalisar da gidan makirci.

 

 

Tags