Pars Today
Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminae ya jaddada bukatar a isarda sakon siyasa na juyin juya halin musulunci a nan Iran ga al-ummar musulmi a ayyukan hajji.
Kungiyar kare hakkin Dan'adam din tana son ganin mahukunta a Saudiyyar ba su kashe Isra, algamgam da wasu mutane hudu da suke tare da ita ba
Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ta yi tofin Allah tsine kan kisan gillar da rundunar kawancen Saudiyya ta yi wa fararen hula a lardin Hudaidah da ke yammacin kasar Yamen.
Wani dan majalisar dokokin Lebanon mai wakiltar Hizbullah ya ce; Shugaba Basshar Assad ya ki yarda da shawarar Saudiyya na yanke alaka da Hizbullah domin Saudiyya ta kashe makudan kudi saboda sake gina Syria
Jami'an tsaron masarautar Saudiyya sun awon gaba da Sheikh Saleh Al Talib daya daga cikin limaman masallacin haramin Makka mai alfarma.
Kwamitin kare hakkokin 'yan kasa a kasar Qatar ya sanar da cewa,a shekarar bana Saudiyya ta haramta wa maniyyata daga kasar ta Qatar zuwa aikin hajji domin sauke farali, saboda dalilai na siyasa.
Dakarun tsaron Yemen sun samu nasarar hallaka sojojin hayar saudiya da dama a wani farmaki da suka kai sansaninsu na jihar Ta'az dake kudu masu yammacin kasar
Kungiyar 'yan ta'addan takfiriyya ta Daesh (ISIS) ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kaddamar da wani hari a kan wani wurin Tsaro a cikin gundumar Qasim a kasar Saudiyya.
Sanarwar amincewar Amurkan ta fito ne daga bakin shugaban kasar Amurkan Donald Trump
Majiyar tsaron kasar Yemen ta shaidawa tashar talabijin din al'alam cewa; Baya ga kashe daruruwan 'yan koren Saudiyyar, an kuma kona da lalata motocin yaki har 44