Pars Today
Shugaban jam'iyyar Labour a kasar Birtaniya Jeremy Corbyn, ya bayyana cewa; sayarwa Saudiyya da manyan makamai da Birtaniya take domin kaddamar da yaki a kan al'ummar kasar Yemen, babban abin kunya ne ga gwamnatin Birtaniya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi, ya bayyana zarge-zargen da Masar da Saudiyya suka yi wa Iran da cewa hankoron haifar da gaba a tsakanin Kasashen musulmi ba maslaha ce gare su ba.
Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya ya yi furucin cin mutunci kan al'ummar Qatar ta hanyar bayyana cewar al'ummar Qatar ba su shige yawan mazauna hanya guda na kasar masar ba.
Piraministan kasar Labnon ya amsa goron gayyatar hukumomin saudiya a wannan Laraba, inda da jijjifin safiyar yau ya tashi daga birnin Bairout zuwa birnin Riyad
Sarki Salman na Saudiyya ya sallami wasu manyan jami'an sojin kasar, ciki har da babban hafsan sojin kasar, Janar Abdel Rahmane ben Saleh al-Bunyan.
Gwamnatin kasar Iraki ta yi watsi da bukatar da gwamnatin Saudiyya ta gabatar mata na ta mika mata wasu 'yan kasar (Saudiyyan) sama da 400 da ake tsare da su saboda samunsu da laifin aikata ayyukan ta'addanci a kasar Irakin.
Jam'iyyun adawa a kasar Jamus sun yi ta suka kan yadda gwamnatin kasar take sayarwa kasar Sa'udiya da kawayenta a yakin Yemen makamai, duk tare da sanin irin laifuffukan yakin da suke aikatawa a kasar.
'Yan majalisar Birtaniyya su ashirin da biyu sun bayyana adawarsu ga ziyarar da Yarima mai jiran gado na Saudiyya zai kai kasar lamarin da ya kara karfafa adawar da wasu kungiyoyi da 'yan siyasar Birtaniyyar suke ga wannan ziyarar.
'Yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun yi watsi da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na tura sojoji zuwa kasar Saudiyya suna masu cewa hakan ya saba wa kudurin da Majalisar ta fitar da ta bukaci gwamnatin ta ci gaba da zama 'yar ba ruwanmu dangane da yakin da Saudiyyan ta kaddamar kan kasar Yemen.
Kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da wani zaman domin yin dubi a kan matsalar rashin ayyukan yi a kasashen musulmi, da kuma samo hanyoyin tunkarar matsalar.