-
Kashoggi : Ana Ci Gaba Da Matsin Lamba Wa Saudiyya
Oct 13, 2018 12:01Kasashen duniya na ci gaba da yin matsin lamba wa Saudiyya akan tayi bayyani kan bacewar dan jaridan nan Jamal Kashoggi wanda ake zargin an kashe shi a karamin ofishin jakadancinta na birnin Santambul a Turkiyya.
-
Rahoton UNICEF Kan Mawuyacin Halin Da Saudiyyah Ta Jefa Kananan Yara A Yemen
Oct 12, 2018 06:03A cikin wannan makon ne hukumar majalisar dinkin duniya da ke kula da ayyukan tallafa wa kananan yara a duniya UNICEF ta fitar da wani rahoto, dangane da irin mawuyacin halin da kananan yara suka samu kansu a ciki a kasar Yemen, sakamakon hare-haren da Saudiyya take kaddamarwa akan al'ummar kasar.
-
Jami'an Turkiyya Suna Da Hujjar Cewa An Kashe Khashoggi A Ofishin Jakadancin Saudiyya - Rahoto
Oct 12, 2018 05:34Wasu rahotanni sun bayyana cewar jami'an kasar Turkiyya sun yi musayen wasu faifan bidiyo da na sauti da suke dauke da hujjojin da suke tabbatar da cewa jami'an Saudiyya sun kashe sanannen dan jaridar nan dan kasar da ke gudun hijira a Amurka, Kamal Khashoggi bayan ziyarar da ya kai karamin ofishin jakadancin kasar a Istanbul.
-
'Yan Majalisar Dattijan Amurka Sun Bukaci Trump Da Ya Bi Kadun Batun Khashoggi
Oct 11, 2018 07:49'Yan majalisar dattijan Amurka 22 mambobin kwamitin harkokin wajen kasar, sun bukaci Trump da ya bi kadun batun bacewar fitaccen marubuci dan kasar Saudiyyah Jamal Khashoggi.
-
Halin Da Ake Ciki Kan Bacewar Dan Jarida Kashoggi
Oct 11, 2018 05:57A halin da ake ciki dai jami'an tsaron Turkiyya sun nuna hoton bidiyo na wasu jami'an Saudiyya da suka zo Turkiya a ranar da Jamal Khashoggi din ya bace.
-
Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Bi Kadun Batun Bacewar Khashoggi
Oct 08, 2018 07:14Majalisar dinkin duniya ta ce ba za ta gum da bakinta ba dangane da batun bacewar dan jaridar nan na kasar Saudiyya da ya yi batan dabo a Turkiya.
-
Erdogan Ya Ce Yana Bin Diddigin Lamarin Dan Jaridar Saudiyya Da Ake Zargin An Kashe A Turkiyya
Oct 07, 2018 17:06Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana cewa yana sanya ido da kuma bin diddigin lamarin dan jaridar kasar Saudiyyan nan, Jamal Khashoggi, wanda ya bace bayan wata ziyara da ya kai karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istanbul inda wasu jami'an Turkiyyan suka ce an kashe shi ne a can din.
-
Turkiya: Ana Zargin An Kashe Khashoggi A Cikin Karamin Ofishin Jakadancin Saudiyya
Oct 07, 2018 07:14Sakamakon farko na binciken da 'yan sandan kasar Turkiya suka gudanar kan bacewar fitaccen dan jaridar Saudiyya mai sukar gwamnati na nuni da cewa, an kashe shi ne a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul.
-
Houthi: Al'ummar Yemen Ba Za Su Mika Wuya Ga Masu Wuce Gona Da Iri Ba
Oct 05, 2018 11:03Shugaban kungiyar 'yan Houthi ta Ansarullah, Abdul Malik Al-Houthi ya bayyana cewar al'ummar kasar Yemen ba za su taba mika kai ga bukatun masu wuce gona da iri, yana mai cewa a shirye ya ke ya tattauna don kawo karshen yakin da aka kaddamar a kasar.
-
UNICEF Ta Yanke Wani Taimako Da Take Bayar Wa A Kasar Yemen
Oct 04, 2018 12:34Hukumar kula da tallafa wa kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta sanar da dakatar da bayar da tallafin wasu kudade ga al'ummar Yemen, saboda matsalolin da take fuskanta.