Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Bi Kadun Batun Bacewar Khashoggi
Majalisar dinkin duniya ta ce ba za ta gum da bakinta ba dangane da batun bacewar dan jaridar nan na kasar Saudiyya da ya yi batan dabo a Turkiya.
Babban jami'in majalisar dinkin duniya mai harhada rahotanni kan hakkokin bil adama da fadar albarkacin baki David Kaye, shi ne ya bayyana hakan a jiya, a lokacin da yake yin tsokaci dangane da batun bacewar Jamal Khashoggi fitaccen marubuci kuma dan jarida na kasar Saudiyya a karamin ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya da ke birnin Istanbul na Turkiya.
David Kaye ya ce, idan dai har ta tabbata cewa Jamal Khashogi an kashe shi ne kamar yadda ake zato, to majalisar dinkin duniya za ta dauki matakin bin kadun lamarin domin gano wadanda suke da hannu a cikin batun.
Manyan kafofin yada labarai da dama sun bayar da rahotanni da ke nuni da cewa an kashe Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya ne a ranar Talata da ta gabata
Khashoggi dai fitaccen marubuci ne wanda yake tare da gwamnatin Saudiyya, amma daga shekarar da ta gabata ya fara sukar salon siyasar yarima mai jiran gadon sarautar kasar Muhammaf Bin Salman, haka nan kuma yana adawa da yakin da Saudiyya take kaddamarwa a kan al'ummar kasar Yemen, wanda kuma saboda haka ne ya bar kasar ta Saudiyya domin tsira da rayuwarsa.