Pars Today
Ofishin babban mai shigar da kara na gwanatin kasar saudiyyah, ya bukaci da a zartar da hukuncin kisa kan wasu 'yan farar hula 5 a kasar, daga cikinsu har da fitacciyar mai rajin kare hakkokin mata a kasar.
Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce sojoji da dakarun sa kai na Ansarullah sun kame yankuna da dama da su ke a yammacin kasar
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Saudiyya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi musayar wuta da wani dan bindiga a garin al-Bakiryah da ke kusa da birnin Riyadh fadar mulkin kasar.
Wani malamin Ahlu sunnah dan kasar Saudiyay ya mutu a hannun jami'an tsaron kasar, sakamakon azbatrawar da suka yi masa.
Wasu daga cikin al'ummar kasar Tunisiya sun gudanar da jerin gwano zuwa ofishin jakadancin Saudiya dake birin Tunis domin nuna rashin amincewarsu kan hana visa
Ma'aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ta yi Allah wadai kan ta'addancin da kawancen Saudiya ya kaiwa motar Bas din dake dauke da yara 'yan makaranta a lardin Dahyan na jahar Sa'ada da ya yi sanadin mutuwar 39 da kuma jikkatar wasu 51 na daban.
Wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen, ya yi sanadiin mutuwar yara 'yan makaranta a kalla 39 tare da jikkata wasu mutane 48 na daban a arewacin kasar ta Yemen.
Kakakin sojojin Kasar Yemen ya sanar da cewa; Sun kai hari da jirgi maras matuki akan cibiyar jiragen sama ta sarki Khalid da ke gundumar Asir a kudancin Saudiyya
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta a lardin Sa'adah da ke arewacin kasar Yamen, inda suka kashe mutane biyu ciki har da karamin yaro guda.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tsananin damuwarta kan yadda mahukuntan Saudiyya suke ci gaba da tsare 'yan adawar kasar.