Jiragen Saman Yakin Masarautar Saudiyya Sun Kashe Mutane A Kasar Yamen
Aug 01, 2018 11:54 UTC
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta a lardin Sa'adah da ke arewacin kasar Yamen, inda suka kashe mutane biyu ciki har da karamin yaro guda.
Rahotonni daga Yamen suna bayyana cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta a cikin daren jiya Talata kan lardin Sa'adah da ke shiyar arewacin kasar Yamen, inda suka kashe fararen hula biyu, kuma daya daga cikinsu karamin yaro ne tare da jikkata wani mutum guda na daban.
Hare-haren wuce gona da irin jiragen saman yakin masarautar Saudiyya da na kawayenta kan Yamen suna ci gaba da janyo hasarar rayukan mutane tare da wurga al'ummar kasar cikin mummunan yana yi musamman na karancin abinci da rashin magunguna.
Tags