-
Assad Ya Musanta Maganar Hadin Gwiwa Tsakanin Rasha Da Isra'ila Wajen Kawo Hari Siriya
Jun 10, 2018 06:27Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad yayi watsi da wasu rahotanni da suke cewa akwai hannun kasar Rasha ko kuma tana da masaniyya kan hare-haren baya-bayan nan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kawo kasar kafin a kawo su.
-
Rikici Ya Sake Kunno Kai Tsakanin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Da Suke Kasar Siriya
Jun 05, 2018 02:04Sakamakon sabanin mahanga a tsakanin jagororin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar Siriya musamman bangaren 'yan siyasarsu hakan ya janyo wasu da dama sun yi murabus daga kan mukamansu.
-
Kabilun Siriya Sun Sanar Da Goyon Bayansu Ga Shugaba Asad Da Kin Amincewa Da Sojojin Waje
Jun 04, 2018 13:51Sama da kabilun kasar Siriya 70 ne suka sanar da goyon bayansu ga shugaban kasar Bashar al-Asad kamar yadda kuma suka sanar da kirkiro wani sansani na gwagwarmaya don fada da kasantuwar Amurka, Faransa da Turkiyya a kasar Siriyan.
-
Shugaban Rundunar Sojin Amurka Ya Gargadi Gwamnatin Kasar Siriya
Jun 01, 2018 09:16Shugaban rundunar sojin kasar Amurka ya gargadi gwamnatin Bashar Asad ta Siriya kan ta nisanci yin amfani da karfi a kan yankunan Kurdawar kasarta da suke shiyar arewa maso gabashin kasar ta Siriya.
-
Siriya : Assad Ya Yi Barazanar Yakar Mayakan Dake Samun Goyan Bayan Amurka
May 31, 2018 05:35Shugaba Bashar al-Assad, na Siriya, ya yi barazanar yin amfani da karfi kan mayakan Kurdawa dana Larabawa dake samun goyan bayan Amurka.
-
Kasar Rasha Ta Sanar Da Mutuwar Jami'an Sojinta Hudu A Kasar Siriya
May 28, 2018 01:59Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa: Jami'an sojinta hudu da suke bada shawarwari kan dabarun yaki a kasar Siriya sun rasa rayukansu a lardin Dire-Zur da ke gabashin kasar Siriya.
-
Shamkhani: Iran ZA Ta Ci Gaba Da Taka Rawa A Siriya Da Kuma Goyon Bayan Gwargwarmaya
May 27, 2018 13:25Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewar Iran za ta ci gaba da taka rawar da take takawa a Siriya da kuma ci gaba da goyon bayan kungiyoyin gwagwarmayar duk kuwa da bukatar kawo karshen hakan da Amurka ta gabatar mata.
-
Amurka Ta Sake Yiwa Siriya Barazana
May 26, 2018 06:30Gwamnatin Amurka ta sake yiwa gwamnatin siriya barazana da mayar da martani mai tsanani a lokacin da ya dace kan abinda ta kira karya yarjejjeniyar tsagaita wuta.
-
Makaman Kariyar Siriya Sun Kakkabo Wasu Makamai Masu Linzami Da Aka Harbo Kusa Da Homs
May 25, 2018 00:56Makaman kariya na kasar Siriya sun kakkabo da kuma dakile wasu hare-hare da makamai masu linzami da aka kawo kan wani filin jirgin sama da ke kusa da garin Homs da ke yammacin kasar, kasa da kwana guda bayan wasu hare-hare da makamai masu linzamin da Amurka da kwayenta suka kai wasu sansanonin sojin kasar a garin Dayr al-Zawr.
-
Siriya Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Kan Ficewar Dakarun Iran Da Na Hizbullah Daga Kasar
May 23, 2018 13:04Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya, Faisal Miqdad yayi watsi da bukatar Amurka na ficewar dakarun Iran da na Hizbullah daga kasar Siriyan yana mai cewa wannan wani lamari ne da gwamnatin Siriya ce za ta dau mataki kansa.