Amurka Ta Sake Yiwa Siriya Barazana
Gwamnatin Amurka ta sake yiwa gwamnatin siriya barazana da mayar da martani mai tsanani a lokacin da ya dace kan abinda ta kira karya yarjejjeniyar tsagaita wuta.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Heather Nauert kakakin ma'aikatar harakokin wajen Amurka a jiya juma'a na cewa tare da kasashen Rasha da Jodan dake a matsayin kasashen dake sanya ido kan yarjejjeniyar tsagaita wuta a yankin, za su gudanar da bincike kan abinda ya faru na baya-bayan, kuma Amurka za ta kadammar da martani mai tsanani kan karya yarjejjeniyar tsagaita wutan da gwamnatin Siriyar ta yi kuma a lokacin da ya dace.
A jiya Juma'a kasashen Rasha da Siriya sun aike da wasiku uku zuwa ga 'yan ta'adda inda suka bukaci su fice daga kauyukan Mahjah, Abta'a, da Da'el dake arewacin jihar Dar'a.
Kafafen yada labarai na kusa da 'yan ta'adda sun bayyana cewa a wasikun an bukaci dukkanin kungiyoyin 'yan ta'addar dake cikin wadannan kauyuka da su ajiye makamansu kuma su amince da yarjejjeniyar sulhu ko kuma su shirya tunakar matakin Soja da gwamnatin za ta dauka kansu