Pars Today
Jim kadan bayan kammala sallar Juma'a ne aka gudanar da Jana'izar Shahidan harin ta'addancin da aka kawo birnin Tehran ranar Larabar da ta gabata tare da halartar duban mutane gami da manyar jami'an gwamnatin Jamhuriyar musulunci ta Iran
Ma'aikatar Harakokin wajen kasar Afirka Ta kudu ta yi alawadai da harin ta'addancin da aka Tehran babban birnin kasar Iran
Majalisar Dokokin kasar Italiya Ta yi shuru na minti guda domin girmama wadanda harin birnin Tehran ya ritsa da su.
Shugaban 'yan sandan birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun kama mutane biyar da ake zargi da hannun cikin harin ta'addancin da aka kai haramin Imam Khumaini (r.a) a jiya yana mai jaddada cewa a halin yanzu dai birnin na Tehran yana cikin aminci babu wata damuwa.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau din nan Alhamis, yayi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga harin ta'addancin da aka kai Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar koda wasa harin ta'addancin da aka kai birnin Tehran ba zai raunana gwiwan al'ummar Iran wajen fuskantar duk wata barazana ba, yana mai jaddada cewar da yardar Allah za a tumbuke tushen ta'addanci.
Komitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya a safiyar yau ya yi shiru na minti guda don tunawa da Iraniyawan da suka rasa rayukansu a hare haren ta'addancin guda biyu da aka kai a nan birnin Tehran
Babban Daraktan yaki da Ta'addanci na Ma'aikatar Leken Asirin Iran ya sanar da kame wasu gungun 'yan ta'adda da suka yi kokarin kai hare-haren ta'addanci a nan birnin Tehran a safiyar yau Laraba.
An bude baje kolin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa karo na 25 a birnin Tehran na kasar Iran, tare da halartar madaba'antu na cikin gida da kuma na kasashen ketare.
Wanda ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran Ayatullah Mohammad Ali Movahedi Kermani ya bayyana cewar wajibi ne shugaban da za a zaba a matsayin sabon shugaban kasar Iran ya zama mai kula da talakawa da kuma kiyaye koyarwar juyin juya halin Musulunci, yana mai jinjinawa al'ummar Iran saboda irin gagarumar fitowar da suka yi.