Duniya Na Ci Gaba Da Allawadai Da Harin Tehran
Majalisar Dokokin kasar Italiya Ta yi shuru na minti guda domin girmama wadanda harin birnin Tehran ya ritsa da su.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Laura Boldrini Shugaban Majalisar Dokokin kasar Italiya a jiya Laraba bayan girmama wadanda harin ta'addanci da aka kai birnin Tehran ya ritsa da su na cewa barazanar ta'addancin da Duniya ke fuskanta na bukatar hadin kai da kuma gaskiya domin kawar da shi.
A bagare guda, Ministan harakokin wajen kasar Italiya Angelino Alfano, Ministan harakokin wajen kasar Birtaniya Sebastian Cortez, Shugaban Majalisar dattijai na kasar Rasha Alexander Lukashenko, Ministan harakokin wajen Austria, Ministan harakokin wajen Faransa, da Shugaban kasar Belarus na daga cikin Shugabanin da suke meka ta'aziyarsu ga Al'ummar kasar Iran da kuma iyalan wadanda harin ya ritsa da su, tare kuma da yin Alawadai da harin ta'addancin da aka kai birnin na Tehran.
A safiyar jiya Laraba ne aka kai hare haren ta'addancin guda biyu a cikin majalisar dokokin kasar Iran a nan Tehran da kuma haramin Imam Khomaini(q) a kudancin birnin Tehran inda mutane 12 suka yi shahada mafi yawansu jami'an tsaro kasar sanna wasu 43 kuma suka jikkata.