Pars Today
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya yi kiran gudanar da zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki na kafin wa'adi, a ranar 24 ga watan Yuni mai zuwa.
Yau Laraba, shuwagabannin kasashen Rasha da Turkiyya da kuma Iran, da wani taron a birnin Ankara na Turkiyya kan batun kasar Siriya.
Kasashen Iran da Turkiyya da kuma Rasha, zasu yi wani taro domin tattauna wa kan batun Siriya.
Taron da kungiyar tarayya Turai ta EU da Turkiyya suka gudanar don warware sabanin dake tsakaninsu, ya watse ba tare da cimma wata matsaya ba.
A yau litinin ne sojojin na Iraki suka isa garin Sinjar da yake a gundumar Nainawa a arewacin kasar saboda hana sojojin Turkiya kutsawa a cikinsa
Ministan harkokin wajen kasar Jamus ya bayyana cewa: Jamus ba zata amince da mamaye garin Afrin na kasar Siriya da sojojin gwamnatin Turkiyya suka yi ba.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar da bayani da a ciki ta bayyana shigar da sojojin Turkiya su ka yi a garin Afrin da cewa mamaya ce da kuma keta hurumin kasar Syria
Mazauna garin na Afrin sun ce Sojojin Turkiya da sojojin 'yanto da Syria, sun fara wawason dukiyarsu bayan da suka shiga cikin birnin
Dakarun Turkiyya da mayakan Siriya dake samun goyan bayan Ankara sun kwace daukacin ikon birnin Afrin tungar mayakan kurdawa da Turkiyyar ke kallo a matsayin 'yan ta'adda.
'Yan ta'addan takfiriyya da suka kafa babbar tunga a yankin Ghouta da ke gabashin birnin Damascus na Syria, sun amince su bar fararen hula su fito daga yankin domin samun kayan agajin da aka kai musu.