Shuwagabannin Kasashen Iran, Turkiyya Da Rasha Na Taro Kan Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29616-shuwagabannin_kasashen_iran_turkiyya_da_rasha_na_taro_kan_siriya
Yau Laraba, shuwagabannin kasashen Rasha da Turkiyya da kuma Iran, da wani taron a birnin Ankara na Turkiyya kan batun kasar Siriya.
(last modified 2018-08-22T11:31:39+00:00 )
Apr 04, 2018 11:18 UTC
  • Shuwagabannin Kasashen Iran, Turkiyya Da Rasha Na Taro Kan Siriya

Yau Laraba, shuwagabannin kasashen Rasha da Turkiyya da kuma Iran, da wani taron a birnin Ankara na Turkiyya kan batun kasar Siriya.

Shuwagabannin kasashen uku zasu tattauna ne kan hanyoyin magance rikicin kasar Siriya.

Kafin hakan shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana taron da mai matukar mahimmanci, bayan farmakin da kasarsa ta kai a yankin AFrin dake arewa maso yammacin Siriya wanda har ya kai ga kwace ikon birnin.

Kasashen Iran da Rasha dai na goyan bayan gwamnatin Bashar Al' Assad, a yayin da Turkiyya ke goyan bayan wani bangare na 'yan tawayen Siriyar.