-
Togo: An Bude Taron Fada Da Ci-Rani
Mar 17, 2018 08:50Taron da aka bude a babban birnin Togo, Lome, shi ne karo na 10 da kasashe masu magana da harshen Faransanci suke yi
-
Sharhi : Taron Kasa Da kasa A Nijar, Kan Dakile Kwararar Bakin Haure Zuwa Turai
Mar 17, 2018 02:25A jiya juma’a ne ministocin cikin gida da na harkokin waje daga kasashen Senegal, Mali, Mauritania, Chadi, Burkina Faso, Ivory Coast, Guinea, Libya, Jamus, Faransa da kuma Italiya, su ka gudanar da taro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar inda suka tattauna kan yadda za a yaki matsalar kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai.
-
Zimbabwe : Juyin Mulki Ne Aka Mini_ Mugabe
Mar 15, 2018 14:50Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya danganta cilasta mashi yin murabus a matsayin juyin mulki.
-
Kamaru : Sojoji Za Su Ci Gaba Da Daukar Mataki A Yammacin Kasa_Biya
Mar 15, 2018 14:07Shugaba Paul Biya na Jamhuriya Kamaru, ya ce dole ne sojojin kasar su ci gaba da matsa kaimi don tabbatar da doka da oda a yankin yammacin kasar na masu amfani da harshen turancin Ingila dake fama da rikici, har sai al'amura tattalin arziki da na jama'a sun daidaita.
-
Isra'ila : Kotu Ta Soke Shirin Korar Bakin Haure 'Yan Afrika
Mar 15, 2018 13:36Kotun kolin Isra'ila ta soke shirin nan na gwamnati da ya tanadi korar dubban bakin haure 'yan Afrika da suka shiga Isra'ilar ba bisa ka'ida ba.
-
Kenya: Za A Kafa Wata Cibiyar Musulunci Domin Dakile Yaduwa Tsatsauran Ra’ayi
Mar 15, 2018 02:08Musulmin kasar Kenya na shirin gina wata cibiyar musulunci wadda za ta mayar da hankali wajen fada da tsatsauran ra’ayin addini a kasar.
-
Hukumar Zaben Saliyo Ta Sanar Da Ranar Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasar
Mar 14, 2018 07:36Hukumar zaben kasar Saliyo ta tsayar da ranar 27 ga watan Maris na da muke ciki a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar bayan da ta sanar da sakamakon karshe na zagayen farko na zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Maris inda babu dan takarar da ya sami kuri'un da ake bukata na ya lashe zaben a zagayen farko.
-
Tattalin Arzikin Arewacin Afirka Ya Bunkasa Da Kashi 4.9
Mar 13, 2018 15:32Bankin bunkasa tattalin arzikin Afirka ya sanar da cewa kashi 4.9 na arzikin kasashen arewacin Afirka ya bunkasa a shekarar 2017 din da ta gabata.
-
Zaben Saliyo: Za a Sake Kirga Kuri'un Wasu Mazabu Kafin Sanar Da Sakamakon Karshe
Mar 13, 2018 07:48Hukumar zaben kasar Saliyo (NEC) ta ce za ta sake kirga kuri'un da aka kada a wasu mazabu 72 na kasar a daidai lokacin da take fatan za ta sanar da sakamakon zaben na karshe a wani lokaci a yau din nan Talata.
-
Zaben Saliyo: Sakamako Na Nuna Cewa Jam'iyyar SLPP Ta 'Yan Adawa Na Kan Gaba
Mar 12, 2018 07:23Sakamakon baya-baya da hukumar zaben kasar Saliyo ta fitar a jiya Lahadi, na zaben shugaban kasar ga aka gudanar a ranar 7 ga watan Maris din nan, na nuni da cewa jam'iyyar SLPP, babbar jam'iyyar adawa ta kasar na kan gaba da kuri'u 15,000 a kan jam'iyyar APC mai mulki.