-
'Yan Sanda Sun Kashe Mutane 5 A D/Congo
Jan 21, 2018 15:39'Yan sanda a D/Congo sun halaka rayukan mutane biyar tare da jikkata wasu da dama na daban a zanga-zangar da aka gudanar ta adawa da Shugaban kasar.
-
Jakadan Equatorial Guinea A MDD Ya Soki Amurka Kan Rashin Neman Gafarar Kasashen Afrika
Jan 19, 2018 14:52Jakadan kasar Equatorial Guinea a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan kasar Amurka saboda rashin neman gafarar kasashen nahiyar Afrika dangane da maganganun cin zarafi da batanci da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan kasashen na Afrika.
-
Tsoffin Jakadun Amurka 78 A Afirka Sun Rubuta Wa Trump Kan Kalamansa Kan Afirka
Jan 17, 2018 14:49A ci gaba da yin Allah wadai da kalaman batanci da shugaban Amurka Donald Trump yayi kan kasashen Afirka, wasu tsoffin jakadun Amurka su 78 da suka taba aiki a kasashe daban-daban na Afirka sun rubuta wa shugaban Amurkan wasika suna masa ishara da irin albarkatu da kwarewar da ake da su a kasashen Afirkan.
-
Shugabar Liberiya Ta Ce Za Ta Tinkarar Jam'iyya Mai Mulki Saboda Korarta Daga Jam'iyyar Da Aka Yi
Jan 17, 2018 14:47Shugabar kasar Liberiya mai barin gado, Ellen Johnson Sirleaf, ta bayyana cewar ta kuduri aniyar tinkarar jam'iyyar Unity Party (UP) mai mulki sakamakon korarta daga jam'iyyar da aka yi a kwanakin baya tana mai bayyana korar na ta a matsayin haramtaccen lamari.
-
Jakadun Kasashen Afirka 54 A MDD Sun Fitar Da Bayanin Yin Tir Da Donald Trump
Jan 13, 2018 08:35Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; Jakadun na kasashen Afirka sun fitar da bayani ne wanda kuma ya kunshi kira ga shugaban na Amurka da ya janye abinda ya furta, ya kuma nemi gafara
-
Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Yi Kakkausar Suka Kan Cin Mutuncin Da Shugaba Trump Ya Yiwa Nahiyar Afirka
Jan 12, 2018 15:38Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kakkausar suka kan cin mutuncin da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yi wa al'ummar Nahiyar Afirka.
-
Shugaban Amurka Ya Ci Zarafin Kasashen Afirika Fiye Da Kima
Jan 12, 2018 08:20Donald Trump Ya ce kasashen Afirka dandazo ne na kazanta, tare da bukatar dakatar da karbar yan hijira daga cikinsu
-
Sojoji Masu Bore A Ivory Coast Sun Kai Hari Da Kona Wani Barikin Soji
Jan 11, 2018 02:18Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun bayyana cewar wasu sojoji masu bore a garin Bouake, gari na biyu mafi girma a kasar, sun kai hari kan wani barikin zaratan sojojin kasar da ake kira da CCDO a garin a daren jiya inda suka kwashi makamai da kuma sanya wuta a wasu bangarori na barikin
-
Equatorial Guinea Ta Rufe Kan Iyakanta Da Kamaru Saboda Yunkurin Juyin Mulki
Jan 08, 2018 07:51Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta rufe kan iyakanta da kasar Kamaru sakamakon zargin juyin mulkin da aka yi kokarin yi wa shugaban kasar, Teodoro Obiang Nguema, a kwanakin baya wanda kuma aka zargi wasu mutane daga Kamaru da hannu ciki.
-
Zababben Shugaban Liberiya Ya Sha Alwashin Fada Da Rashawa Da Cin Hanci A Kasar
Dec 31, 2017 02:24Zababben shugaban kasar Liberiya George Weah ya bayyana cewar kasar Liberiya a shirye take ga masu shirin zuba jari a kasar yana mai shan alwashin fada da rashawa da cin hanci da ya addabi kasar.