Shugaban Amurka Ya Ci Zarafin Kasashen Afirika Fiye Da Kima
(last modified Fri, 12 Jan 2018 11:50:39 GMT )
Jan 12, 2018 11:50 UTC
  • Shugaban Amurka Ya Ci Zarafin Kasashen Afirika Fiye Da Kima

Donald Trump Ya ce kasashen Afirka dandazo ne na kazanta, tare da bukatar dakatar da karbar yan hijira daga cikinsu

Kamfanin dillancin larabun Reuters da ya nakalto labarin ya ce; Shugaban kasar Amurkan, Donald Trump ya ci mutumcin kasashen Afirka din ne a lokacin da yake ganawa wakilan majalisar dokokin kasar biyu -Dick Durbin da -Lindsey Graham, akan sabbin dokokin hijira. 

Trump ya kuma ci gaba da cewa; Saboda me zai sa Amurka ta rika karbar 'yan gudun hijira daga kasashe kamar Haiti da kasashen Afirka, kamata ya yi ta karbi mafi yawancin yan gudun hijira daga Norway."

Tun da Donlad Trump ya fara shugabancin Amurka a ranar 20 ga watan Janairu 2017 ya ke fito da sabbin dokokin hijira zuwa kasar. A tashin farko ya hana kasashen musulmi masu yawa hakkin shiga cikin kasar ta Amurka.