-
Shugaba Buhari Ya Taya George Weah Murnar Nasarar Da Ya Samu A Zaben Shugaban Liberiya
Dec 29, 2017 14:44Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya, ya taya zababben shugaban kasar Liberiya George Weah murnar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar yana mai sake jaddada masa aniyar Nijeriya na ci gaba da karfafa alaka da kasar Liberiyan.
-
Mataimakin Shugaban Liberiya Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Shugaban Kasar
Dec 29, 2017 14:42Mataimakin shugabar kasar Liberiya sannan kuma dan takara a zaben shugaban kasar da aka gudanar Joseph Boakai ya amince da kayen da ya sha a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar yana mai taya shugaban da aka zaba din George Weah murnar nasarar da ya samu.
-
Ana Ci Gaba Kidayen Kuri'un Zaben Shugaban Kasar Liberiya Zagaye Na Biyu
Dec 27, 2017 02:18Rahotanni daga kasar Liberiya sun bayyana cewa an fara kirga kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a jiya Talata tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai da tsohon zakaran wasan kwallon kafa na kasar George Weah.
-
Liberia:Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu
Dec 26, 2017 07:32A yau Talata ne al'ummar kasar Liberia sama da miliyan biyu ke gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin zaben sabon shugaban kasa tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai dan shekaru 73 da haihuwa da George Weah dan shekaru 51 tsohon shahararren dan kwallon kafa na duniya.
-
Tsayin Dakan Kasashen Afirka Wajen Tinkarar Barazanar Trump Kan Qudus
Dec 25, 2017 01:47A daidai lokacin da gwamnatin Amurka take ci gaba da barazana ga kasashen duniya dangane da batun Kudus, kasashen Afirka suna daga cikin kasashen duniya da suka tsaya kyam wajen goyon bayan al'ummar Palastinu da kuma yin watsi da matsayar shugaban Amurkan kan birnin Kudus.
-
Uganda : Majalisa Ta Baiwa Yuseveni Damar Sake Takara
Dec 21, 2017 07:15Majalisar dokokin Yuganda ta amince da yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin bai wa Shugaban kasar Yoweri Museveni, damar sake takara a zaben 2021.
-
'Yan Najeriya 25,000 Ake Tsare Da Su A Libiya _ (NAPTIP)
Dec 20, 2017 07:53Hukumar nan mai yaki da safarar mutane a Najeriyar, watau NAPTIP, ta ce 'yan kasar sama da 25,000 ne ake tsare da su ba bisa ka'ida ba a kasar Libiya.
-
FIDH Ta Zargi Jami'an Tsaron Congo Da Hannu A kisan Jama'a
Dec 20, 2017 07:49Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (FIDH) ta zargi jami'an tsaro kasar Congo da wata kungiyar mayaka da shirya kisan gillar da aka yi a yankin Kasai.
-
Kamaru : An Kashe Jami'an Tsaro Hudu A Kudu Maso Yamma
Dec 19, 2017 07:34Rahotanni daga Kamaru na cewa jami'an tsaron kasar na Jandarma hudu ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai masu a yankin masu magana da harshen turancin Ingilishi a Kudu maso yammacin kasar.
-
Nijar Na Bikin Cika Shekaru 59 Da Ta Zama Jamhuriya
Dec 18, 2017 07:20A Nijar a wannan Litinin ce kasar ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 59 da zama Jamhuriya.