Nijar Na Bikin Cika Shekaru 59 Da Ta Zama Jamhuriya
A Nijar a wannan Litinin ce kasar ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 59 da zama Jamhuriya.
A wannan karon dai birnin Tawa ne ke karbar bakluncin bikin, wanda aka ma taka ''Tawa Sakola''.
A yayin bikin dake gudana yanzu haka shugaban kasar Mahamadu Isufu zai kaddamar da manyan ayyuka na kawatawa da fadada birane kamar yadda ake yi a ko wacce shekara a yayain zagayowar irin wannan bikin.
A shekaru uku da suka gabata shugaban kasar ya jagoranci irin wannan bukukuwa a biranen Dosso, Maradi da Agadas sai kuma bana a Tawa.
Bikin na bana dai ya sha babban da wadanda suka gabata inda shugabannin kasashen Afrika biyar ne ake kyautata zaton za su halarci bikin da suka hada na Najeriya Muhammadu Buhari, da takwarorinsa na Burkina Faso, Chadi, Mali da kuma Mauritaniya.