Liberia:Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26723-liberia_ana_gudanar_da_zaben_shugaban_kasa_zagaye_na_biyu
A yau Talata ne al'ummar kasar Liberia sama da miliyan biyu ke gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin zaben sabon shugaban kasa tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai dan shekaru 73 da haihuwa da George Weah dan shekaru 51 tsohon shahararren dan kwallon kafa na duniya.
(last modified 2018-08-22T07:01:12+00:00 )
Dec 26, 2017 07:32 UTC
  • Liberia:Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu

A yau Talata ne al'ummar kasar Liberia sama da miliyan biyu ke gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin zaben sabon shugaban kasa tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai dan shekaru 73 da haihuwa da George Weah dan shekaru 51 tsohon shahararren dan kwallon kafa na duniya.

Duk wanda ya samu nasara zai karbi ragamar tafiyar da gwamnatin kasar ta Laberiya daga hannun Ellen Johnson Sirleaf 'yar shekaru 73 wadda ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar kasa a nahiyar Afirka.

Wasu dai na ganin hukumar zaben Liberia ta yi gaggawar sake shirya zaben zagaye na biyu , amma wasu kuma na ganin cewa abin da hukumar zaben ta yi yayi daidai, saboda hakan shi zai sanya 'yan kasar su shiga cikin sabuwar  shekara da sabon shugaban kasa.

Kafin hakan dai, mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai  kuma dan takara a zaben ya bukaci hukumar zabe da ta soke zaben zagaye na biyu, saboda a cewarsa an tabka kura-kure da zagaye na farko.