Mataimakin Shugaban Liberiya Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Shugaban Kasar
(last modified Fri, 29 Dec 2017 18:12:12 GMT )
Dec 29, 2017 18:12 UTC
  • Mataimakin Shugaban Liberiya Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Shugaban Kasar

Mataimakin shugabar kasar Liberiya sannan kuma dan takara a zaben shugaban kasar da aka gudanar Joseph Boakai ya amince da kayen da ya sha a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar yana mai taya shugaban da aka zaba din George Weah murnar nasarar da ya samu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar Mr. Joseph Boakai ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da yayi da daruruwan magoya bayansa da suka taru a helkwatar jam'iyyarsu inda yace tuni ya buga wa Mr. George Weah waya don taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben, yana mai cewa wajibi ne a yi aiki wajen hada kan al'ummar Liberiya wacce ta ke gaba da dukkan kowa.

Mr. Boakai ya ce duk da dai ya sha kaye a zaben, to amma a kullum fatan da yake da shi shi ne ci gaban kasar Liberiya yana mai cewa a shirye yake yayi aiki tare da sabon shugaban kasar a duk wani fagen da shugaban ya ke ganin zai iya ba da tasa gudummawar.

A jiya ne dai hukumar zaben kasar Liberiyan ta sanar da sakamakon farko-farko na  zaben da ya ba wa George Weah din nasarar inda ya samu kashi 61.5 na kuri'un da aka kada lamarin da ya ba shi damar zama shugaban kasar da zai gaji shugaba mai ci uwargida Ellen Johson-Sirleaf wacce ta shugabanci kasar na  tsawon shekaru 12.