Uganda : Majalisa Ta Baiwa Yuseveni Damar Sake Takara
Dec 21, 2017 07:15 UTC
Majalisar dokokin Yuganda ta amince da yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin bai wa Shugaban kasar Yoweri Museveni, damar sake takara a zaben 2021.
'Yan majalisa 315 suka amince da shirin, yayin da 62 suka nuna rashin amincewa.
Shirin dai zai bayar da dama ga wadanda suka haura shekaru 75 tsayawa takara a zaben shugaban kasa.
Hakan dai zai baiwa wanda kuma shugaba Yoweri Museveni dan shekaru 73 damar sake takara a babban zaben na shekara 2021.
Mista Museveni wanda ya shafe fiye da shekaru 30, yana mulki zai iya ci gaba da rike madafun iko har zuwa shekara ta 2031.
Tags