-
'Yan Adawar Gambiya: Babu Wata Kotu Da Za Ta Soke Zaben Adamar Barrow Da Aka Yi
Dec 24, 2016 13:18Gamayyar 'yan adawan kasar Gambiya sun yi watsi da sanarwar da kotun kolin kasar ta yi na fara sauraran karar da shugaban kasar Yahya Jammeh ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar inda suka ce babu wata kotu a duniyar nan da ta isa ta sauya nasarar da dan takararsu Adamar Barrow ya samu a zaben 1 ga watan Disamban da aka gudanar.
-
An Sanar Da Karshen Cutar Zazzabin Shawara A Kasar Angola
Dec 24, 2016 13:17Gwamnatin kasar Angola ta sanar da kawo karshen cutar shawara da ta balle a kasar wacce kuma ta yi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 400 a duk fadin kasar.
-
Rahoton Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Kan Kisan Fararen Hula a Afirka Ta Tsakiya
Dec 21, 2016 13:05Wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun fitar da wani rahoto dangane da kisan wasu fararen hula 23 da aka yi a kasar.
-
Wasu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Rikicin Da Ya Barke A Kongo
Dec 20, 2016 14:53Rahotanni daga Jamhuriyar Demokradiyar Congo na cewa alal akalla wasu fararen hula su biyu sun rasa rayukansu kana wasu sun sami raunuka sakamakon bude wuta da sojoji suka yi kan mutanen da suke ci gaba da zanga-zangar nuna adawa ga shugaba Joseph Kabila na kasar.
-
Mauritaniya: Jama'a Na Neman A Zartar da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Ci Zarafin Ma'aiki
Dec 18, 2016 09:13Dubban al'umma ne suka gudanar da jerin gwano a birnin Nuwakshot na kasar Mauritaniya, da ke nemana zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya ci zarafin ma'aiki (SAW) a kasar.
-
ECOWAS Ta Nada Buhari A Matsayin Babban Mai Shiga Tsakani A Rikicin Gambiya
Dec 18, 2016 02:00Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta zabi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a matsayin babban mai shiga tsakani don magance takaddamar siyasar da ta kunno kai a kasar Gambiya bayan kin amincewar da sakamakon zaben shugaban kasar da shugaba Yahya Jammeh yayi.
-
Kungiyar AU Ta Nuna Damuwa Kan Yiyuwar Shigowar 'Yan Ta'adda Nahiyar Afirka
Dec 15, 2016 07:45Kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya bayyana tsananin damuwarsa dangane da yiyuwar dawowar dubun dubatan 'yan ta'adda nahiyar Afirka bayan shan kashin da suke fuskanta a Siriya da Iraki.
-
'Yan Super Falcons Na Nijeriya Sun Yi Zanga-Zanga A Gaban Majalisar Dokoki Saboda Kin Biyansu Albashinsu
Dec 14, 2016 07:38'Yan kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nijeriya, Super Falcons, sun gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokin kasar zuwa fadar shugaban kasa don nuna rashin jin dadinsu dangane da rashin biyansu hakkokinsu da ba a yi ba bayan da suka ciwo kofin Afirka a kasar Kamaru.
-
Jam'iyyar Shugaba Jammeh Ta Shigar Da Kara Kan Sakamakon Zaben Shugaban Kasar
Dec 14, 2016 07:37A daidai lokacin da alamu suke nuni da rashin nasarar kokarin shiga tsakanin da kungiyar ECOWAS ta tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka take yi don magance rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar Gambiya, jam'iyyar APRC mai mulki a kasar ta shigar da kara tana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar ta sanar inda ta ce shugaba Yahya Jammeh ya sha kaye.
-
Gwamnatin Kasar Masar Ta Karbi Tallafin Dalar Amurka Miliyon 500 Daga Bankin Raya Kasashen Afrika
Dec 13, 2016 15:30Gwamnatin kasar Masar ta karbi tallafin dalar Amurka miliyon 500 daga bankin raya kasashen Afrika, wato African Developmen Bank.