An Sanar Da Karshen Cutar Zazzabin Shawara A Kasar Angola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15667-an_sanar_da_karshen_cutar_zazzabin_shawara_a_kasar_angola
Gwamnatin kasar Angola ta sanar da kawo karshen cutar shawara da ta balle a kasar wacce kuma ta yi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 400 a duk fadin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:26+00:00 )
Dec 24, 2016 13:17 UTC
  • An Sanar Da Karshen Cutar Zazzabin Shawara A Kasar Angola

Gwamnatin kasar Angola ta sanar da kawo karshen cutar shawara da ta balle a kasar wacce kuma ta yi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 400 a duk fadin kasar.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce sakamakon gagarumin shirin rigakafi na gaggawa bisa daukin Majalisar Dinkin Duniyada aka gudanar a kasar an sami nasarar dakile cutar shawara din da ta bullo din.

Sanarwar ta kara da cewa tun watan Yunin da ya gabata har ya zuwa yanzu ba a sake samun bullar wannan cutar ba, lamarin da ya ke nuni da cewa an sami nasarar dakile cutar ta shawara wacce ta barke a kasar Angolan a watan Disamban shekarar bara. Cutar dai  ta  faro ne daga babban birnin kasar Luanda, sannan kuma ta bazu zuwa larduna 16 daga cikin 18 na kasar har zuwa kasar Demokradiyyar Kongo da ke makwabtaka da Angolan.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana wannan bullar shawarar a matsayin mafi muni a duk fadin duniya a wannan zamani da muke ciki.