Pars Today
Majalisar koli ta malaman addinin musulunci a kasar Algeria ta fitar da fatawar haramta hijira zuwa kasashen turai ba bisa ka'aida ba.
Gwamnatin kasar Algeria ta bada sanarwar gano wani rumbun ajiyar makamai da kayakin yaki a kan iyakar kasar da kasar Mali.
Shugaban kasar Algeria Abdul-aziz Butaflika ya aike da wasika zuwa ga shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani inda a cikinta yake taya shi murnar cika shekaru 39 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda 15 a sassa daban daban na kasar a cikin watan Janairun da ya gabata.
Priministan kasar Algeria ya yi kira ga kasashen Afrika da su yi hattara da kungiyar Daesh kada ta shigo kasashensu bayan an fatattakesu a kasashen Siria da Iraqi.
Fira ministan Aljeriya ya yi zargin cewa: Daga kasar Maroko ce ake fataucin muggan kwayoyi zuwa cikin kasarsa da ma sauran kasashen da suke yankin Arewacin Afrika.
Kasashen Aljeriya da Libiya sun cimma yarjejeniyar ci gaba da gudanar da aiki tare a yankunan da suke tsakanin kasashen biyu masu dauke da albarkatun man fetur da iskar gas.
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da cewa: A cikin shekarar da ta gabata ta 2017, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda fiye da casa'in.
Jami'an tsaron kan iyaka na kasar Algeria sun kara tsananta yaki da fasa-kwabrin makamai zuwa cikin kasar daga kan iyakokin kasar.
Gwamnatin Aljeriya ta fara karfafa shirinta na fitar da siminti zuwa kasashen waje domin rage dogaro da man fetur a harkar tattalin arzikin kasar.