An Bukaci Kasashen Afrika Su Yi Hattara Da Shigowar Kungiyar Daesh Kasashensu
(last modified Mon, 29 Jan 2018 11:47:45 GMT )
Jan 29, 2018 11:47 UTC
  • An Bukaci Kasashen Afrika Su Yi Hattara Da Shigowar Kungiyar Daesh Kasashensu

Priministan kasar Algeria ya yi kira ga kasashen Afrika da su yi hattara da kungiyar Daesh kada ta shigo kasashensu bayan an fatattakesu a kasashen Siria da Iraqi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ahmed Oyahia yana fadar hada a taron shuwagabannin kasashen Afrika AU karo na 30 da ake gudanar da shi a halin yanzu a kasar Ethiopia.

Priministan ya kara da cewa fatattakar mayakan Daesh da kuma sauran kungiyoyin yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraqi wani ci gaba ne sosai ga kasashen yankin, amma akwai barazanar da wadannan kungiyoyi suke wa sauran kasashen Larabawa ko na Afrika har yanzun. Don haka akwai bukatar ko wace kasa ta yi hattara da shigowarsu zuwa kasashensu.

Priministan ya kammala da cewa akwai yan ta'adda yan asalin kasashen Afrika da suka yi yaki tare da Daesh a kasashen Iraqi da Siriya kimani 6000.