-
Ministan Tsaron Iran: Amurka Tana Amfani Da 'Yan Ta'adda Don Cimma Muradinta
Sep 09, 2018 07:30Ministan tsaron kasar Iran, Birgediya Janar Amir Hatami, ya bayyana cewar Amurka tana amfani da duk wata dama da take da ita ciki kuwa har da amfani da kungiyoyin 'yan ta'adda don cimma manufa da muradinta ba tare da la'akari da muradin sauran kasashen duniya ba.
-
Obama Yayi Kakkausar Suka Ga Siyasar Gwamnatin Trump
Sep 08, 2018 10:28Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, yayi kakkausar suka ga yadda shugaban kasar Donald Trump yake gudanar da mulkinsa yana mai cewa hakan ne ma zai sa a samu karin fitowar mutane yayin zabe na gaba da nufin kawar da wannan gwamnatin.
-
Rouhani: Iran Ba Ta Kiyayya Da Wata Kasa Face Amurka, "Isra'ila" Da 'Yan Amshin Shatansu
Sep 08, 2018 10:28Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar a halin yanzu Iran ba ta kiyayya da wata kasa in ban da Amurka, haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan amshin shatansu, don haka sai ya ce: Al'ummar Iran ta hanyar hadin kai da aiki tare za su yi nasara kan makiyansu.
-
Trump Ya Ce Zai Sanya Karin Haraji Kan Wasu Kayakin China Da Ke Shigowa Amurka
Sep 08, 2018 06:54Shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Jumma'a ya bada sanarwan cewa zai kara sanya wasu kayakin da ake shigo da so kasar Amurka daga kasar China haraji.
-
'Yan Ta'adda Da Dama Suna Ta tserewa Daga Lardin Idlib Na Syria
Sep 07, 2018 19:04'Yan ta'addan takfiriyyah suna ci gaba da tserewa daga lardin Idlib na kasar Syria, a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ta Syria take shirin fara kaddamar da wani gagarumin farmaki a kansu.
-
Nasrallah: Amurka da 'Isra'ila' Sun Gaza Wajen Cimma Manufarsu A Gabas Ta Tsakiya
Sep 06, 2018 16:41Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah, ya bayyana cewar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila sun sha kashi cikin dukkanin makirce-makircen da suka kulla don cimma bakar aniyarsu a yankin Gabas ta tsakiya.
-
Amurka Ta Gargadi Kasashen Rasha Da Iran Kan Harin Da Suke Son Kaiwa Yan Ta'adda A Idlib
Sep 04, 2018 06:34Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gargadi kasashen Rasha da Iran kan anniyarsu ta tallafawa gwamnatin kasar Siriya ta kwace tungar yan ta'adda na karshe a kasar wato garin Idlib.
-
Amurka Ta Yanke Dukkan Tallafin Da Take Bawa Palasdiwa Yan Gudun Hijira
Sep 01, 2018 06:31Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bada sanarwan dakatar da tallafin kudade da ta saba bawa yan gudun hijira Palasdinawa karkashin kungiyar nan ta UNRWA.
-
Kungiyar OIC Ta Yi Allawadai Da gasar Cin Zarafin Musulunci A Holland
Aug 31, 2018 06:31Kungiyar kasashen muuslmi ta yi Allawadai da kakkausar murya, dangane da gasar zanen batunci a kan addinin muslunci da wasu masu kiyayya da addinin muslunci suka shirya a kasar Holland.
-
Shugaban Amurka Ya Ki Amincewa Da Fitar Da Sakon Yabo Kan John McCain Da Ya Mutu
Aug 27, 2018 12:27Shugaban kasar Amurka ya ki amincewa da fitar da bayani daga fadar shugabancin kasar kan mutuwar John McCain sanata a Majalisar Dattijan Kasar mai wakiltan jihar Arizona.