Obama Yayi Kakkausar Suka Ga Siyasar Gwamnatin Trump
Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, yayi kakkausar suka ga yadda shugaban kasar Donald Trump yake gudanar da mulkinsa yana mai cewa hakan ne ma zai sa a samu karin fitowar mutane yayin zabe na gaba da nufin kawar da wannan gwamnatin.
Tsohon shugban na Amurka ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a jami'ar Illinois a jihar Chicago na Amurka inda ya bayyana cewar a halin yanzu dai Amurkan tana cikin wani loakci mai matukar muhimmanci da hatsari ne.
Barrack Obama ya ce gwamnatin Trump ta lalata kyakkyawar alaka da dangantaka da ke tsakanin Amirkan da aminanta sakamakon irin siyasar da take gudanarwa, don haka ya kirayi al'ummar Amurka da su fito yayin zaben shugaban kasar mai zuwa don sauya wannan yanayi da ake ciki.
Wannan dai ba shi ne karon farko da shugaba Obaman yake sukar siyasar gwamnatin Trump din ba saboda irin yadda ta ke ci gaba da cutar da muradan Amurkan a ciki da wajen kasar.