-
Mafi yawan Amurkawa na adawa da hana musulmci shiga cikin kasar.
Feb 19, 2017 11:09Bisa wani sabon Jin Ra'ayin Al'umma da aka gudanar, mafi yawan Amurkawa sun bayyana adawar su da hana Musulmi shiga cikin kasar Amurka.
-
Shugaban Trump Na Amurka Ya Kori Wani Jigo A Majalisar Tsaron Kasar Daga Aiki Don Sukarsa
Feb 19, 2017 06:25Fadar white Hause ta bada sanarwan korar wani jigo a majalisar tsaron kasar daga aiki saboda sukar da yayi wa shugaba Donal Trump da iyalansa kan yadda suke tafiyar da kasar.
-
Wani Bangare Na Laifuffuka Da Wuce Gona Da Irin Amurka A Kasar Siriya
Feb 18, 2017 05:56Kakakin Rundunar Tsaron Amurka (Centcom) Manjo Josh Jacques ya bayyana cewar rundunar sojin Amurkan ta yi amfani da sama da albarusai 5000 da aka kera su daga karfen uranium din da aka sarrafa a wasu hare-hare guda biyu da suka ce sun kai kan wasu tankokin man fetur na kungiyar Da'esh (ISIS) a lardunan Deir Zur da Hasaka na kasar Siriya a watan Nuwamban 2015, duk kuwa da alkawarin da suka yi a baya na cewa ba za su sake amfani da wannan mugun sinadari ba.
-
Trump Zai Maye Gurbin Dokar Hana Musulmi Shiga Kasar Amurka Da Wata Sabuwar Doka
Feb 17, 2017 12:08Shugaban kasar Amurka Donal Trump zai kafa wata sabuwar doka ta hana musulmi shiga Amurka a mazaunin wacce aka yi watsi da ita.
-
Sayyid Nasrallah: Wajibi Ne A Hukunta Saudiyya Da Amurka Saboda Kirkiro Da'esh
Feb 16, 2017 18:04Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar wajibi ne a hukunta gwamnatocin Saudiyya da Amurka saboda kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) da kuma goyon bayanta.
-
Hukumomin Leken Asirin Amurka Suna Boye Wasu Bayanan Sirri Wa Trump Saboda Rashin Yarda Da Shi
Feb 16, 2017 18:04Rahotanni na nuni da cewa hukumomin leken asirin Amurka suna boye wasu bayanan sirri masu muhimmanci wa shugaban kasar Donald Trump saboda rashin yarda da shi da kuma tsoron cewa akwai yiyuwar ayi wasa da kuma fitar da su.
-
Shugaban Kasar Venezuela Ya Ja Kunnen Amurka Kan Siyasarta Kan Kasarsa
Feb 16, 2017 18:03Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya ja kunnen Amurka da cewa kasarsa za ta mayar da martani mai kaushin gaske da duk wani kokarin wuce gona da iri da Amurkan za ta yi kan kasarsa.
-
Amurka Ba Zata tilasta Ba Kan Samar Da Kasashen Palestinu Da Isra'ila Ba
Feb 15, 2017 05:52Amurka ta ce ba zata tilasta ba akan batun samar da kasashen Palestunu da Isra'ila ba a yankin Gabas ta Tsakiya da kasahen duniya da dama suka dade suna fata.
-
Wani Dan Majalisar Dokokin Amurka Ya Caccaki Siyasar Trump Ta Kin Jinin Musulmi
Feb 14, 2017 17:22Wani dan majalisar dokokin Amurka ya yi kakkausar suka a kan salon siyasar shugaban kasar Donald Trump ta kin musulmi da kuma baki a cikin kasar ta Amurka.
-
Mai Bawa Shugaban Kasar Amurka Shawara Kan Harkokin Tsaro Ya Yi Murabus
Feb 14, 2017 12:21Mai bawa shugaban kasar Amurka Donal Trump shawara kan harkokin tsaron kasa Michael Flynn ya yi murabus daga matsayinsa bayan zargin cewa ya gana da jakadan kasar Rasha a Amurka.