Mafi yawan Amurkawa na adawa da hana musulmci shiga cikin kasar.
Bisa wani sabon Jin Ra'ayin Al'umma da aka gudanar, mafi yawan Amurkawa sun bayyana adawar su da hana Musulmi shiga cikin kasar Amurka.
Sabon jin ra'ayin Al'ummar ya tabbatar da cewa kashi 65% na Amurka na adawa da matakin Shugaba Trump na hana musulmi shiga cikin kasar Amurka yayin da kashi 26% kacal ne suka goyin bayan wannan shiri.
Kasar Amurka dai na daga cikin kasashen da suka gino da 'yan gudun hijra sabanin kasashen masu al'adu da Tahiri, domin ita kasar, 'yan gudun hijra na kasashen Turai ne da suka yi hijra kasar sanadiyar matsalar siyasa, sabinin ra'ayi da sauransu suka gina ta.
A irin Kasar, daukan irin wannan mataki ba abu ba ne mai sauki saboda idan har 'yan kasar suka amince da wannan mataki to shakka babu, dokar za ta shafi kowa da kowa.
Mafi yawan Amurkawa na ganin cewa sassauci da saukaka Al'adu gami Addini shine babban gimshikin kafa kasar Amurka.