-
MDD: Mutane 50,000 Sun Gudu Daga Garin Bosso Na Nijar Saboda Tsoron Boko Haram
Jun 08, 2016 01:15Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCHR) ta bayyana tsananin damuwarta dangane da makomar kimanin mutane 50,000 da suka gudu daga garin Bosso na jamhuriyar Nijar sakamakon munanan hare-haren kungiyar Boko Haram.
-
'Yan Boko Haram Sun Sake Kwace Garin Bosso Na Jamhuriyar Nijar
Jun 06, 2016 13:47Rahotanni daga kasar Nijar suna nuni da cewa 'yan kungiyar nan ta Boko Haram sun sake kwace garin Bosso da ke kan iyakan kasar da Nijeriya a yau din nan Litinin bayan da sojojin kasar suka kwace shi daga hannunsu a shekaran jiya.
-
Nijar Ta Kaddamar Da Wani Shiri Na Amfani Da Jirage Mara Matuki Wajen Fada Da Boko Haram
May 31, 2016 00:54Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewar mahukunta a kasar sun kaddamar da wani shiri na amfani da jirage marasa matuka a kokarin da gwamnatin kasar take yi na fada da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da suka addabin kasar da sauran makwambtanta.
-
Sojojin Nijar Sun Hallaka Wasu 'Yan Boko Haram A Kasar
May 29, 2016 11:28Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa sojojin kasar sun sami nasarar hallaka wani adadi na 'yan kungiyar Boko Haram a wani ba ta kashi da ya gudana tsakanin bangarorin biyu.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Hallakar Babban Mai Kera Bomb Wa Boko Haram
May 23, 2016 14:17Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da mutuwar daya daga cikin shugabanni kana kwararrun masu kera wa kungiyar Boko Haram ta kasar bama-baman da suke kai hare-haren ta'addanci a kasar lamarin da ake ganinsa a matsayin wata gagarumar ci gaba a kokarin da ake yi na ganin bayan 'yan ta'addan.
-
Fadar Shugaban Nijeriya: 'Yar Chibok Za Ta Gana Da Buhari A Yau Alhamis
May 19, 2016 00:57Fadar shugaban Nijeriya ta sanar da cewa a yau Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari zai gana da daya daga cikin 'yan matan Chibok din nan da aka kwato daga hannun Boko Haram, a daidai lokacin da ake fatan za a samu bayanin da zai ga ceto sauran 'yan matan sama da 200 da Boko Haram din suka sace sama da shekaru biyu da suka wuce.
-
Shugaba Hollande Ya Bayyana Cewar Har Yanzu Boko Haram Barazana Ce Ga Afirka
May 15, 2016 00:54Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce duk da cewa an ci karfin kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram a Nijeria, to amma har ya zuwa yanzu kungiyar tana a matsayin babbar barazana ga nahiyar Afirka.
-
Gwamnatin Kamaru Ta Sanar Da Kwato Yara Da Mata Daga Hannun Boko Haram
May 15, 2016 00:52Gwamnatin kasar Kamaru ta sanar da samun nasarar kwato wani adadi mai yawa na kananan yara da mata daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram wadanda suka yi garkuwa da su.
-
Ministan Tsaron Nijeriya: Sojojin Na Shirin Korar Boko Haram Daga Sambisa
May 01, 2016 12:31Ministan tsaron Nijeriya Alhaji Mansur Dan'Ali ya bayyana cewar sojojin Nijeriya sun gama shirin da ake bukata wajen tarwatsa dukkanin sansanoni da maboyar 'yan kungiyar Boko Haram da suke dajin nan na Sambisa
-
Sojojin Nijeriya Sun Sami Gagarumar Nasara A Kan 'Yan Boko Haram
Apr 17, 2016 23:31A ci gaba da kokarin da sojojin Nijeriya suke yi na kawo karshen kungiyar nan ta Boko Haram, sojojin sun sanar da wata gagarumar nasarar da suka samu a kan 'yan kungiyar biyo bayan wani hari da suka kai daya daga cikin maboyan 'yan kungiyar.