-
Wasu Iyayen 'Yan Matan Chibok Sun Gano 'Ya'yansu Cikin Faifan Bidiyon Boko Haram
Apr 13, 2016 23:24Wasu iyayen 'yan matan makarantar sakandaren nan ta Chibok da ke jihar Bornon Nijeriya sun bayyana cewar sun gano 'ya'yansu da kungiyar Boko Haram ta sace shekaru biyu da suka gabata cikin wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a shekaran jiya Talata.
-
Iyayen Matan Chibok: 'Yar Kunar Bakin Waken Karamu Ba 'Yar Mu Ba Ce
Mar 31, 2016 12:38Wasu daga cikin iyayen 'yan matan sakandaren garin Chibok da ke jihar Bornon Nijeriya sun musanta ikirarin da yarinyar nan da jami'an tsaron kasar Kamaru suka kama a kwanakin baya tana shirin kai harin kunar bakin-wake ta yi na cewa tana daga cikin 'yan matan Chibok din da Boko Haram suka sace kimanin shekaru biyu da suka gabata, inda suka ce lalle ba 'yarsu ba ce.
-
Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nijar Guda Shida A Yankin Difa
Mar 31, 2016 12:17Ma'aikatar cikin gidan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa wasu sojojin kasar guda shida sun mutu kana wasu uku kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kwanton bauna da wasu mahara da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai musu a kusa da garin Difa da ke kudu maso gabashin kasar.
-
Kamaru: Ana Gudanar Da Binciken Lafiya 'Yar Kunar Bakin Waken Da Tace Tana Daga Cikin 'Yan Chibok
Mar 28, 2016 23:23Hukumomi a kasar Kamaru sun fara gudanar da bincike na likitanci da kuma ba da magani ga 'yar kunar bakin waken nan da jami'an tsaron kasar suka kama a kwanakin baya wacce kuma ta yi ikararin cewa tana daga cikin 'yan makarantar sakandaren garin Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace kimanin shekaru biyu da suka gabata.
-
Nijeriya Za Ta Tura Iyayen 'Yan Matan Chibok Kamaru Don Tantance 'Yan Kunar Kakin Wake
Mar 27, 2016 10:36Gwamnatin Nijeriya ta sanar da aniyarta ta tura wasu daga cikin iyaye da mutanen garin Chibok da a baya 'yan kungiyar Boko Haram suka sace wasu 'yan mata 'yan makaranta a garin zuwa kasar Kamaru domin tantance ko wata 'yar kunar bakin waken da aka kama a can din tana daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace kamar yadda ta yi ikirari.
-
Sojojin Nigeria Sun Kwato Garin Kala Balge Daga Hannun Boko Haram
Mar 24, 2016 23:59Rundunar sojan Nijeriya ta sanar da fatattakan 'yan kungiyar Boko Haram daga garin Kala Balge da ke jihar Borno da kuma kwace ikon garin daga hannun, bugu da kari kan kubutar da mutane kimanin 520 da suke hannun 'yan ta'addan.
-
Helkwatar Sojin Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Shekau
Mar 24, 2016 23:32Helkwatar tsaron Nijeriya ta yi watsi da sabon faifai bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren da take kai wa 'yan kungiyar da nufin ganin bayansu duk kuwa da halin damuwar da Shekau din ya nuna yana ciki a sabon faifan bidiyon.
-
'Yan Sandan Taraba Sun Tabbatar Da Kama Kwamandojin Boko Haram 2
Mar 24, 2016 04:49Rundunar 'yan sandan jihar Taraba a Nijeriya ta tabbatar da kama wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram guda 2 wadanda aka jima ana nemansu inda ta ce tuni ta mika su ga sojoji a jihar.
-
Kotu Ta Dage Shari'ar Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya Alex Badeh
Mar 14, 2016 13:53Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta sanar da ranar Laraba mai zuwa wato 16 ga watan Maris din nan da muke ciki a matsayin ranar za'a fara shari'ar da za a yi wa tsohon Babban hafsan sojin Nijeriya, Air Marshal Alex Badeh, mai ritaya saboda zargin halalta kudin haramun da ake masa.
-
Gwamnati: "Shigar Nijeriya Kawancen Musulunci Ba Shi Da Alaka Da Addini"
Mar 08, 2016 02:16Ministan harkokin wajen Nijeriya Mr. Geoffrey Onyama ya bayyana cewar sabanin korafe-korafen da wasu suke yi, shigar Nijeriya rundunar hadin gwiwar kasashen Musulmi karkashin jagorancin Saudiyya don 'fada da ta’addanci' ba shi da alaka da wani addini.