Helkwatar Sojin Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Shekau
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2890-helkwatar_sojin_nijeriya_ta_mayar_da_martani_ga_sabon_faifan_bidiyon_shekau
Helkwatar tsaron Nijeriya ta yi watsi da sabon faifai bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren da take kai wa 'yan kungiyar da nufin ganin bayansu duk kuwa da halin damuwar da Shekau din ya nuna yana ciki a sabon faifan bidiyon.
(last modified 2018-08-22T06:58:02+00:00 )
Mar 24, 2016 23:32 UTC
  • Helkwatar Sojin Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Shekau

Helkwatar tsaron Nijeriya ta yi watsi da sabon faifai bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren da take kai wa 'yan kungiyar da nufin ganin bayansu duk kuwa da halin damuwar da Shekau din ya nuna yana ciki a sabon faifan bidiyon.

Helkwatar tsaron ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Rabe Abubakar ya sanya wa hannu a jiya Alhamis inda ya ce: Helkwatar tsaron ta Nijeriya tana sanar da cewa sojojin Nijeriya za su ci gaba da yakar kungiyar ta Boko Haram don kammala nasarorin da aka samu, ba tare da da la'akari da abin da ya zo cikin faifan bidiyon (na Shekau) ba.

Sanarwar ta kara da cewa tana kiran al'ummar Nijeriyan da su yi watsi da faifan bidiyon don kuwa yana iya zama wani makirci ne da 'yan ta'addan suka kulla don wasa da hankulan mutane don su damar cutar da su a duk lokacin da suka kawo hari. Don haka suka kirayi al'umma da su kara yin taka tsantsan, a daidai lokacin da sojoji suke cikin shirin ci gaba da hare-haren da suke kai wa 'yan kungiyar da nufin kawo karshensu.

A jiya ne dai kungiyar Boko Haram din ta fitar da wani sabon faifan bidiyo na kusan mintuna takwas wanda ke nuna shugabanta, Abubakar Shekau yana magana sai dai ba cikin kuzarin da aka saba ganinsa a baya ba da nufin tabbatar da wa 'yan kungiyar da cewa yana raye.