Sojojin Nigeria Sun Kwato Garin Kala Balge Daga Hannun Boko Haram
Rundunar sojan Nijeriya ta sanar da fatattakan 'yan kungiyar Boko Haram daga garin Kala Balge da ke jihar Borno da kuma kwace ikon garin daga hannun, bugu da kari kan kubutar da mutane kimanin 520 da suke hannun 'yan ta'addan.
A cikin wata sanarwa mai sanye da sa hannun kakakin rundunar sojin Kanar Sani Usman Kukasheka, rundunar sojin ta ce a wasu sabbin hare-hare da sojojin suka kaddamar a ranar Talatar da ta gabata sun sami nasarar kawar da dukkan 'yan Boko Haram da suke yankin na Kala Balge bayan sun tarwatsa sansanoninsu na ba da horo, masana'antun da suke kera makamai bugu da kari kan rumbunansu na ajiye makamai da kayayyakin yaki.
Har ila yau sanarwar ta ce sojojin sun sami nasarar kubutar da mutane 309 da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su bugu da kari kan kashe 'yan Boko Haram 22 da kuma fatattakan sauran daga garuruwan Wumbi, Tinish, Tilem, Malawaji da sauran kauyukan da suke yankin.
Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai sojojin na Nijeriya suna ci gaba da samun nasarori a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram a kokarin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar take yi na kawo karshen Boko Haram din da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin kasar ta Nijeriya.