Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nijar Guda Shida A Yankin Difa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3208-boko_haram_sun_kashe_sojojin_nijar_guda_shida_a_yankin_difa
Ma'aikatar cikin gidan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa wasu sojojin kasar guda shida sun mutu kana wasu uku kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kwanton bauna da wasu mahara da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai musu a kusa da garin Difa da ke kudu maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 31, 2016 12:17 UTC
  • Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nijar Guda Shida A Yankin Difa

Ma'aikatar cikin gidan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa wasu sojojin kasar guda shida sun mutu kana wasu uku kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kwanton bauna da wasu mahara da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai musu a kusa da garin Difa da ke kudu maso gabashin kasar.

Rahotanni daga kasar sun ce ma’aikatar cikin gidan kasar ta Nijar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ‘yan Boko Haram sun yi wa sojojin kasar kwanton bauna a lokacin da suke sintiri a yankin na Diffa dake kusa da iyaka da Nijeriya inda sojoji 6 suka mutu wasu uku kuma suka sami raunuka.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta Nijar na ci gaba da kokarinta na ganin bayan ayyukan ta’adanci a yankin Diffa dake iyaka da kasashen Nijeriya da Chadi .

Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan kungiyar ta Boko Haram suke kai hari yankin na Difa ba lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutane kasar baya ga raunata wasu da dama.

Nijar dai tana daga cikin kasashen biyar na yankin da suka hada da Nijeriya, Kamaru, Chadi da Benin wadanda suke ci gaba da hada karfi da karfe wajen ganin bayan kungiyar ta Boko Haram wacce ta addabe su.