-
Buhari Ya Gana Da Shugabannin Majalisun Nijeriya Don Dinke Barakar Da Ta Kunno Kai
Mar 16, 2018 11:09A wani abin da ake gani a matsayin kokarin dinke barakar da ta kunno kai tsakanin fadar shugaban Nijeriya da majalisun kasar, shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriyar ya gana da shugabannin majalisun tarayyar kasar su biyu a daren jiya.
-
Buhari Ya Jinjinawa Kokarin Shugaban Kasar Ghana Na Fada Da Rashawa Da Cin Hanci
Mar 06, 2018 16:38Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya jinjinawa kokarin da gwamnatin kasar Ghana take yi wajen fada da rashawa da cin hancin yana mai bayyana aniyarsa na hada kai da shugaban kasar wajen fada da wannan annoba da ta damu kasashen biyu.
-
Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Sanar Da Tura Karin Jiragen Sama Don Neman 'Yan Matan Dapchi
Feb 26, 2018 05:46Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta kara tura jiragen sama da sauran na'urorin bincike zuwa yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriyan don ci gaba da neman 'yan matan makarantar mata ta Dapchi da suka bace bayan wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai makarantar a makon da ya wuce.
-
Buhari: Gwamnati Tarayya Za Ta Sayar Da Kadarorin Da Ta Kama A Matsayin Na Sata
Feb 20, 2018 05:15Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana cewar gwamnatin tarayyar kasar za ta sayar da dukkanin kadarorin da ta kama, da suka hada da kayayyaki da filaye da gidaje da sauran su, sannan ta gano cewa na sata ne wadanda kuma aka rasa masu shi da sanya kudin cikin asusun gwamnati.
-
Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaron Kasa Kan Yanayin Tsaro A Nijeriya
Feb 12, 2018 17:57Sakamakon ci gaba da matsaloli na tsaro da ake fuskanta a Nijeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya jagoranci wani zama na majalisar tsaron kasar a fadarsa da ke Abuja don tattauna batutuwan tsaron da kuka daukar matakan da suka dace wajen magance su.
-
Shugaba Buhari Ya Kori Wasu Manyan Alkalai Biyu Daga Aiki
Feb 10, 2018 05:46Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kori wasu alkalai guda biyu na babbar kotun tarayyar kasar daga aiki, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.
-
Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Tana Neman Kakakin Babangida Ruwa A Jallo
Feb 06, 2018 17:36Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa tana neman kakakin tsohon shugaban kasar Janar Ibrahim Babangida (rtd), wato Kassim Afegbua, ruwa a jallo saboda fitar da sanarwar bogi da kuma bata suna abin da zai iya janyo rigima da tashin hankali a Nijeriyan.
-
Osinbajo: Abin Da Ya Damu Buhari Shi Ne Cika Alkawarin Da Yayi Wa 'Yan Nijeriya Ba Zaben 2019 Ba
Jan 25, 2018 17:44Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar babban abin da shugaban Nijeriyan, Muhammadu Buhari, ya sa a gaba a halin yanzu shi ne kokari wajen ganin ya cika alkawarin da yayi wa 'yan kasar a lokacin yakin neman zaben 2015 ba wai batun zaben shekara ta 2019 ba.
-
Buhari Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Hare-Haren Mahara A Kasar Nan Ba Da Jimawa Ba
Jan 23, 2018 05:13Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana cewar nan ba da jimawa ba hare-haren da wasu 'yan bindiga da ake cewa makiyaya ne suke kai wa wasu sassa na kasar zai kawo karshe sakamakon irin matakan da gwamnatinsa take dauka.
-
Sheikh El-Zakzaky Ya Gana Da Manema Labarai A Karon Farko
Jan 13, 2018 15:57Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar shugaban kungiyar Harkar Musulunci a kasar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya gana da manema labarai karon farko tun bayan da aka kama shi shekaru biyu da suka gabata inda ya bayyana cewar yana nan a raye kuma lafiyar lau inji kafafen watsa labaran.